logo

HAUSA

Kwamandan rundunar gabashin Libya ya sanar da niyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar

2021-11-17 11:02:11 CRI

Kwamandan rundunar gabashin Libya ya sanar da niyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar_fororder_211117-Libya-Fa'iza

Kwamandan rundunar sojin Libya dake gabashin kasar wato Khalifa Haftar, ya sanar da kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar.

Yayin wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin, Khalifa Haftar ya ce kasarsu na kan wasu gabobi biyu, daya ta ‘yanci da zaman lafiya, yayin da dayar ta kasance ta tashin hankali da rikici. Kuma al’ummar kasar ne kadai za su iya zabar tafarkin da suke so.

Ya ce yana jinjinawa yunkurin kasashe kawayen Libya da suka taimaka wajen ingiza damarmakin demokradiyya da kuma bukatar gudanar da zabukan shugaban kasa da na ’yan majalisa, a matsayin mafita daya tilo ga rikicin kasar.

Ya kara da cewa, yana sanar da burinsa na tsayawa takara ba don neman iko ko matsayi ba, sai dai don jagorantar al’ummar kasar zuwa ga ci gaba da kwanciyar hankali.

Ana sa ran Libya za ta gudanar da babban zabenta a ranar 24 ga watan Disamban bana, a matsayin wata hanya da taron tattauna batun siyasar kasar da MDD ta dauki nauyi ya gabatar da zummar tabbatar da zaman lafiya a kasar. (Fa’iza Mustapha)