logo

HAUSA

Yan sandan Nijeriya sun ceto mutane 11 da aka sace a yankin Delta

2021-11-17 10:48:19 CRI

Yan sandan Nijeriya sun ceto mutane 11 da aka sace a yankin Delta_fororder_211117-Nigerian police-Fa'iza

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce jami’anta dake sintiri sun ceto wasu mutane 11 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Delta ta kasar.

Bright Edafe, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Delta ya shaidawa manema labarai a birnin Warri cewa, gungun ’yan bindiga sanye da kayan soja, sun kai hari kan wata motar bas dake kan hanyar Ozoro zuwa Ughelli ta jihar, inda suka yi awon gaba da fasinjoji, a ranar Lahadi da dare.

Sai dai, ’yan sanda sun farwa ’yan bindigar bayan samun kiran neman agaji, inda suka shiga dazukan dake kusa, domin ceto mutanen kuma suka cimma nasara bayan sa’o’i kalilan.

Ya ce jami’an sun killace wurin tare da shiga dazukan, bayan ’yan bindigar da ake zargin sun gano hakan, sai suka tsere suka bar mutanen 11.

’Yan sanda sun kuma gano motar da aka yi amfani da ita wajen kai harin, inda kuma aka matse kaimi wajen kamo ’yan bindigar da suka tsere.

Hare-haren ’yan bindiga ya zama babbar barazanar tsaro a fadin Nijeriya, lamarin da ke kaiwa ga kisa da sace-sacen mutane. (Fa’iza Mustapha)