Burodin Nang da ake samarwa a Xinjiang ya karyata karairayin kasashen yamma
2021-11-17 21:35:30 CRI
A yau ne, ake sa ran burodin Nang da aka yi bisa ga bukatunku zai tashi kuma ana sa ran ya isa Rasha nan da kwanaki 5. To, na gode sosai! Yadda wani dan kasuwa a Khorgos, Xinjiang, na kasar Sin, ya tattauna da abokan cinikin Rasha ta kafar bidiyon wayar hannu. A wannan rana ne aka fitar da wata motar dakon kaya dauke da burodin Nang miliyan 1 daga tashar iyakar kasa ta Khorgos, inda ta kama hanyar zuwa kasar Rasha a karon farko, sannan ta shiga kasuwar Turai a karon farko.
A yau, jihar Xinjiang ta zama wata muhimmiyar hanya ta mu'amala tsakanin kasashen da ke kan hanyar ziri daya da hanya daya. Ga shaidu, batun "aikin tilas", "kisan kare dangi" da sauran karairayi da makiyan kasar Sin dake kasashen yamma suka kirkira suna da rauni kuma sun zama tamkar wasan yara.(Ibrahim)