logo

HAUSA

“Dakin Girki na Yaki da Sankara” dake dumama zuciyoyin masu fama da ciwon sankara da iyalansu

2021-11-17 16:40:42 cri

A wani karamin lungu da ke birnin Nanchang na lardin Jiangxi dake kudu maso gabashin kasar Sin, akwai wani wurin dafa abinci na musamman, a duk lokacin da ake cin abinci, mutane masu lafuzza iri-iri suna haduwa a nan, suna yin girki tare, kuma a wurin suna nuna kwarin gwiwa ga juna, da samu niyyar ci gaba da zaman rayuwarsu. Wannan wurin dafa abinci bango daya ne tsakanin sa da asibitin ciwon sankara na lardin Jiangxi. A cikin ‘yan shekaru da yawa da suka wuce, yana ta samar da sauki ga marasa lafiya dake kwance a asibiti da iyalansu ta hanyar yin girki, hakan yasa ake kiran shi da "Dakin Girki na Yaki da Sankara" wanda ya yi suna a wurin.

A shekarar 2003, Xiong Gengxiang da mijinta suna yi da sayar da soyayyar waina siririya, a wannan lungu da ke birnin Nanchang na lardin Jiangxi. Wata rana, wasu ma'aurata biyu sun zo rumfar Xiong Gengxiang tare da dansu mara lafiya, kuma sun tambaye ta ko za ta iya ba su aron kuka da murhu don yin girki, saboda "dansu yana son cin abincin da mahaifiyarsa ke dafawa." Ko shakka babu, Xiong Gengxiang ta yarda da bukatar su.

“Dakin Girki na Yaki da Sankara” dake dumama zuciyoyin masu fama da ciwon sankara da iyalansu_fororder_抗癌厨房1

"Akwai wani wurin da ake iya yin girki a lungun da ke kusa da asibitin ciwon sankara", wannan labari ya bazu a tsakanin mutane cikin sauri, kuma mutane da yawa sun rika zuwa rumfar Xiong Gengxiang suna aron kuka da murhunta don dafa abinci. Domin biyan bukatun marasa lafiya da iyalansu na dafa abinci, Xiong Gengxiang da mijinta sun rufe rumfar sayar da soyayyar waina.

Iyalan majinyatan da suka zo yin girki sun yi bakin ciki da samu wannan labari, don haka suka gabatar da shawarar biyan Xiong Gengxiang kudi don amfani da wurin. Domin kwantar da hankulansu, da kuma biyan kudin ruwa da na kwal, sai Xiong Gengxiang da mijinta sun yarda da karbar kudin Sin RMB centi 5 kacal, kwatankwacin Naira 32 don soya abinci guda. Ya zuwa shekarar 2016 farashin ya tashi zuwa kudin yuan 1 wato kimanin Naira 64.

Wannan “Dakin girki na fama da sankara” na karbar yuan 1 kacal, kuma ba a taba rufewa ba a tsawon shekaru 18, ko a yanayin sanyi ko na zafi. Yana ba wa mutane masu bukata kayan girki da abubuwan da ake karawa cikin abinci kyauta, kuma yana karbar mutane fiye da 10,000 don dafa abinci a nan a ko wace shekara.

Shekaru da yawa da suka wuce, Xiong Gengxiang da mijinta ​​sun tsufa, gashin kansu yana komawa fari, kuma kumburi yana mamaye fuskokinsu, amma sun dage kan gudanarwar da “Dakin Girki na Yaki da Sankara”, don kara kwarin gwiwa ga marasa lafiya da iyalansu na ci gaba da rayuwa.

Xiong Gengxiang ta ce, "Muna son samar wa marasa lafiya da iyalansu wani gida mai dumi da kauna na gajeren lokaci."

A cikin 'yan shekarun nan, labarin Xiong Gengxiang da mijinta ​​da kuma "Dakin Girki na Yaki da Sankara" yana ta burge mutane da yawa, har hakan ya sa suka samu yabo daga bangarori daban daban.

A watan Fabrairun shekarar 2018, an shigar da Xiong Gengxiang da mijinta a cikin "Jerin mutane masu kirki na kasar Sin". A watan Fabrairun shekarar 2021, an ba su lambar yabo ta "Mutanen da suka burge Sinawa". A watan Nuwamba na shekarar 2021 kuma, an zabe su a matsayin abun koyi a fannin dabi'a na kasa…

Yanzu “Dakin Girkin” ya canza. A karkashin taimakon gwamnatin wurin, an lika tangaran a bangon dakin dafa abincin, kuma an gina marufi maras launi a saman lungun da dakin ke ciki, kana kuma an cika rumfuna da tukwane da kwanonin da mutane masu kauna suka ajiye.

“Dakin Girki na Yaki da Sankara” dake dumama zuciyoyin masu fama da ciwon sankara da iyalansu_fororder_抗癌厨房2

Kuang Fengxiu, wacce ke kula da mijinta marar lafiya, ta shafe fiye da watanni 10 tana yin girki a cikin "Dakin Girki na Yaki da sankara". Ta ce, a da idan an yi iska da ruwan sama, ruwan sama ya kan sauka a cikin tukunyar, don haka ta kan rike da laima yayin da take dafa abinci. Amma, yanzu halin ya samu kyautatuwa. Ba za ta sha wahala daga iska da ruwan sama ba. Kuang Fengxiu ta ce, duk wadannan sun karfafe ta da mijinta, wajen ci gaba da rayuwarsu.

A kowace rana da karfe 4 na safe, Xiong Gengxiang da mijinta suna amfani da itace don kunna murhun gawayi bayan sun tashi. Da karfe 9 na safe, dakin girkin na maraba da rukunin farko na baki, har sai bako na karshe ya tashi da karfe 8 ko 9 na dare.... Wannan shi ne yadda take faruwa a “Dakin Girki na Yaki da Sankara” a kowace rana.

Mijin Xiong Gengxiang ya ce, kusan shekaru 20 ke nan, “mu da iyalan majinyatan ba mu iya rabuwa da juna, idan sun rabu da mu, za su sha wahala wajen ci abinci, idan muka bar su, mu ma za mu ji kadaici.”

Babu wani abinci mai tsada a cikin “Dakin Girki na Yaki da Sankara”, amma kowane irin abinci yana cike da soyayya daga wajen iyaye, ko 'ya'ya, ko miji da mata da sauransu, wadanda suke cike da fatan iyalan dake fuskantar wahalhalu, na sake komawa zaman rayuwarsu na yau da kullum.

Xiong Gengxiang da mijinta sun ce, mu talakawa ne, kuma abin da za mu iya yi shi ne, mu ci gaba da bude wannan dakin girki, ta yadda marasa lafiya da iyalansu za su iya ci gaba da jin dumi da dadi a nan.