Hadin Kan Sha’anin Sararin Samaniya Na Ingiza Zumuncin Sin Da Afrika
2021-11-17 21:24:53 CRI
Daga Amina Xu
Abokaina, kuna amfani da tauraron dan Adam na sadarwa wajen ziyartar shafukan Intanet da buga waya da sauraron radiyo. Kasar Sin ce, ta taimakawa Najeriya wajen harba wasu taurarin dan Adam dinta, alal misali a shekarar 2007, Sin ta taimakwa Najeriya wajen harba tauraron dan Adam na sadarwa na farko daga cibiyar harba tauraron dan-Adam na Xi Chang, wanda ya biya bukatar jama’ar Najeriya ta fuskar sadarwa da sauraron radiyo da Intanet da sauransu. Ban da wannan kuma, Sin ta harba tauraron dan Adam mai lamba 1R daga cibiyar Xi Chang. Wannan tauraron dan-Adam ba ma kawai ya ragewa kasashen Afrika kudin da suke biya ta fannin sadar, kuma yana taka muhimmiyar rawa a fannin ciniki ta yanar gizo da ba da ilmi ta Intanet da ingiza tattalin arziki na yanar gizo. Kudin zamani da gwamnatin Najeriya ta gabatar a kwanan baya wato E-Naira na da alaka da wannan tauraro.
Ban da fannin sadarwa, kimiyyar Sin a fannin sararin samaniya na kuma taimaka muku wajen kama shirye-shiryen talibijin. A watan Agusta na shekarar 2017, Sin ta fara shirinta na taimakawa kauyuka fiye da dubu 10 na ganin suna kama shirye-shiryen talabijin na zamani. A waccan shekara ina aiki a Najeriya, kuma na halarci bikin kaddamar da aikin gwaji a wannan fanni a kauyen Hulumi dake karkarar birnin Abuja. Lokacin da na shiga wani gida a wurin, na ga yara na kallo shirye-shiryen TV da suka kama ta nau’urar tauraron dan-Adam, suna kara ilminsu daga shirye-shiyren talibijin. Wadannan shirye-shirye masu inganci, sun baiwa ‘yan Najeriya musamman ma yara wani dandali na fahimtar abubuan dake faruwa a sassan duniya. Ya zuwa yanzu, wannan shiri na shafar kasashen Afrika fiye da 20, inda kauyuka fiye da dubu 10 suna kama shirye-shiryen talibijin na zamani. Matakin da ya samu karbuwa daga jama’ar Najeriya matuka, har wani shugaban kauye dake jihar Osun ya rubuta wata wasika don nuna godiya. Duk wadannan abubuwa shaidu ne ga dankon zumuncin dake tsakanin Sin da Najeriya.
Ban da hadin kan Sin da Najeriya a fannin sararin samaniya, Sin tana hadin kai da kasashen Afrika daban-daban a wannan fanni, alal misali cibiyar harhada tauraron dan Adam da aikin gwaji dake Masar wato AIT, da shirin taimakawa kauyuka fiye da dubu 10 kama shirye-shiryen talabijin na zamani da kuma tauraron dan Adam na sadarwa na farko na Aljeriya da sauransu. Ban da wannan kuma, kimiyyar Sin a fannin tauraron dan Adam na zamani na taimakawa nahiyar Afrika wajen dakile cutar COVID-19. Shirin taimakawa kauyuka fiye da dubu 10 kama shirye-shiryen talabijin na zamani, ya gabatar da shirye-shiryen ba da ilmi da kandagarkin cutar, darektan ofishin yammacin Afrika na UNESCO ya taba bayyana cewa, wadannan shirye-shirye ba ma kawai sun taimakawa matasan Afrika wajen samun ilmi mai kyau ba, suna kuma taimakawa wajen kara kafin kandagarki.
Ban da ba da taimako wajen harba tauraro dan-Adam ko samar da na’urorin kama shirye-shiryen talibijin na zamani, Sin na taimakawa Afrika wajen horar da masana a wannan fanni. Cibiyar kimiya da fasaha ta yankin Asiya-Pacific dake karkashin MDD da aka kafa a jami’ar zirga-zirgar sararin sama da kimiyyar sararin samaniya ta Beijing, ta kan ba da taimako wajen ba da horo a wannan fannin ga daliban kasashen Afrika. Bayanai na nuna cewa, tun daga shekarar 2014, cibiyar ta horar da dalibai 32 daga kasashen Afrika 8 ciki hadda Aljeriya da Masar da Habasha da Kamaru da Mozambique da Najeriya da Sudan ta hanyar ba su guraben karo ilimi kyauta.
Kungiyar nazarin harkokin sararin samaniya ta Afrika wato Space In Africa (SIA) ta ba da rahoto cewa, a shekarar bara yawan kudin da nahiyar Afrika ta kashe a fannin nazarin sararin samaniya ya ninka sau daya. An yi hasashen cewa, a cikin shekaru 3 masu zuwa, yawan taurarin dan Adam da nahiyar za ta harba zuwa sararin samaniya, zai kai 110. Wani jami’in AU mai kula da aikin nazarin sararin samaniya ya ce, Sin ta zama sahihiyar kawa ga Afrika wajen cimma burin nazarin sararin samaniya. A shekarun baya-bayan nan, Sin na kara habaka hadin kai da kasashen Afrika a wannan fanni, matakin da ya taimakawa kasashen wajen ingiza karfinsu na dogaro da karfin kansu a wannan fanni.
Saboda haka, an iya ganin cewa, hadin kan Sin da Afrika a wannan fanni ya ingiza zumuncinsu, Temidayo Oniosun wanda ya kafa kungiyar SIA ya ce, kasashen Afrika na fatan kara hadin kai da kasar Sin a fannin kimiyya da fasahar sararin samaniya. Wannan batu haka yake, dangantakar dake amfanawa juna da kawo moriyar juna na samun karbuwa daga jama’ar kasashen biyu, kuma zai taka rawa ga taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da za a gudanar a karshen wannan wata da muke ciki, yayin taron za a gabatar da muradun hadin kan Sin da Afrika nan da shekarar 2035, ba shakka, akwai makoma mai haske a fannin nazarin sararin samaniya a cikin wannan muradu. (Amina Xu)