logo

HAUSA

Rahoto: Iyalan dubban sojoji Amurkawa na fuskantar kamfar abinci

2021-11-17 11:50:46 CRI

Rahoto: Iyalan dubban sojoji Amurkawa na fuskantar kamfar abinci_fororder_211117-Food insecurity-Saminu

Wani rahoton baya bayan nan ya nuna cewa, kimanin sojojin Amurka 160,000 na fuskantar karancin abincin ciyar da iyalan su, sakamakon kamfar abincin da ake tanada a runbunan tsumi na kasar.

Rahoton na cibiyar Feeding America, ya nuna yadda Amurkawa, ciki har da sojoji ke fuskantar kamfar abinci. Kaza lika alkaluman kididdigar cibiyar ta bara ma, ta nuna yadda kaso 29 bisa dari na kananan sojojin Amurka suka sha fama da karancin abinci.

Rahoton ya ce, cikin shekaru da dama, miliyoyin Amurkawa daga sassa daban daban na rayuwa, na fama da karancin ababen bukata na yau da kullum, lamarin da jami’in hulda da gwamnatin kasar na cibiyar ta Feeding America Mr. Vince Hall, ya bayyana a matsayin mummunan abun kunya. (Saminu)