logo

HAUSA

Ganawar bidiyo ta farko tsakanin Sin da Amurka za ta ci gaba da bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu

2021-11-16 20:54:10 CRI

Ganawar bidiyo ta farko tsakanin Sin da Amurka za ta ci gaba da bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu_fororder_中美-3

A safiyar yau ne agogon birnin Beijing na kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta hanyar bidiyo.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wasu ka'idoji guda uku da za su daidaita alakar Sin da Amurka: Na farko, mutunta juna. Na biyu shi ne zaman tare cikin lumana. Kana na uku, hadin gwiwar samun nasara tare.

Xi Jinping ya kuma bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su mai da hankali kan wasu muhimman abubuwa guda hudu a halin yanzu: Na farko, nuna nauyin da ke wuyansu a matsayinsu na manyan kasashen duniya, da jagorantar al'ummomin duniya wajen yin hadin gwiwa don tunkarar manyan kalubale. Na biyu shi ne inganta mu’amala a kowane mataki da kuma sassa daban-daban bisa tsarin daidaito da samun moriyar juna. Na uku shi ne daidaita bambance-bambance da batutuwa masu muhimmanci ta hanya mai ma'ana, don ganin dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ba ta tabarbare ko shiga wani yanayi ba. Na hudu shi ne karfafa hadin kai da hadin gwiwa kan manyan batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyya-shiyya, don tabbatar da daidaito da adalcin tsarin kasa da kasa.(Ibrahim)