logo

HAUSA

Shugabannin Sin Da Amurka Sun Yi Ganawa Ta Bidiyo A Karo Na Farko

2021-11-16 13:27:29 CRI

Shugabannin Sin Da Amurka Sun Yi Ganawa Ta Bidiyo A Karo Na Farko_fororder_hoto

Da sanyin safiyar yau Talata bisa agogon Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden sun tattauna da juna ta kafar bidiyo.

Yayin tattaunawar tasu, shugaba Xi Jinping ya ce,

“Gaishe ka, malam Biden, wannan shi ne karo na farko da muke ganawa ta kafar bidiyo, ina farin cikin ganawa da abokina. A halin yanzu, Sin da Amurka na kan wata gaba mai muhimmanci ta ci gaba, yayin da duniya ke fuskantar kalubale da dama. A matsayinmu na kasashe mafiya karfin tattalin arziki, kuma masu kujerar naki a kwamitin sulhu na MDD, akwai bukatar Amurka da Sin da mu kara tuntubar juna, da hadin gwiwa, kana kowacce cikinmu ta tafiyar da harkokinta na cikin gida yadda ya kamata. A lokaci guda kuma, mu sauke nauyin dake wuyanmu, na fuskantar batutuwan da suka shafi duniya, mu hada hannu domin tabbatar da burin zaman lafiya da ci gaba a duniya. Wannan buri ne na bai daya na al’ummomin kasashen biyu da ma sauran sassan duniya.

Kuma, ana bukatar kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka, domin ci gaban kasashen, da kuma kare zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, ciki har da lalubo ingantattun hanyoyin tunkarar kalubale kamar na sauyin yanayi da annobar COVID-19. Ya kamata Sin da Amurka mu rika mutunta juna, tare da gudanar da hulda cikin kwanciyar hankali da hadin gwiwar moriyar juna. Bugu da kari, a shirye nake in hada hannu da shugaba Biden wajen cimma matsaya guda, tare da daukar matakan inganta dangantakarmu. Domin yin hakan zai kyautata muradun jama’ar kasashen biyu da fatan al’ummun duniya baki daya.”

A nasa bangare kuwa, shugaban kasar Amurka Joseph Robinette Biden ya ce,

“Ina farin cikin ganawa da kai, da fatan za mu yi shawarwari ba tare da boye komai ba, kamar yadda muka yi a baya. A gani na, a matsayin shugabannin kasashen Amurka da Sin, muna da nauyin kare zaman lumana, gami da gasar dake tsakanin kasashen biyu. A ganina, ya kamata mu kafa dandalin tattaunawa, domin cimma matsayi daya kan wasu batutuwa, da kuma warware sabanin dake tsakaninmu yadda ya kamata, yayin da muke hada kai kan fannonin dake shafar moriyar juna, musamman ma kan batun sauyin yanayi, da ma sauran manyan batutuwan kasashen duniya. Dangantakar dake tsakanin kasashenmu, ba kawai tana yin tasiri ga kasashenmu ba ne, har ma, tana yin tasiri ga sauran kasashen duniya.”

Rahotanni sun tabbatar da cewa, akwai sauran manyan jami’ai guda biyar na kasar Sin, da ma manyan jami’ai guda biyar na kasar Amurka, wadanda suka halarci wannan taro na ganawa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)