logo

HAUSA

Sin: Ganawar bidiyo da shugabannin Sin da Amurka suka yi gwaji ne na dangantakar Sin da Amurka

2021-11-16 19:59:25 CRI

Sin: Ganawar bidiyo da shugabannin Sin da Amurka suka yi gwaji ne na dangantakar Sin da Amurka_fororder_1116

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, taron farko ta kafar bidiyo tsakanin Sin da Amurka da ya gudana a yau, wani gwaji ne na dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka a wani muhimmin lokaci, kuma yana da matukar muhimmanci ga ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a mataki na gaba. Shugaba Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun amince su ci gaba da tuntubar juna ta hanyoyi daban-daban.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, kasar Sin na bin ka'idoji, wadanda za a iya takaita su a matsayin ka'idoji guda uku da shugaba Xi Jinping ya ambata a yau: mutunta juna, zaman tare cikin lumana, da hadin gwiwar samun nasara tare.(Ibrahim)