logo

HAUSA

Ya dace a tabbatar da adalci da daidaito yayin da ake aiwatar da sauye sauye a ayyukan kwamitin tsaron MDD

2021-11-16 14:15:18 CRI

Ya dace a tabbatar da adalci da daidaito yayin da ake aiwatar da sauye sauye a ayyukan kwamitin tsaron MDD_fororder_211116-Saminu 3-MDD

Yayin zaman babban zauren MDD na 76 a jiya Litinin, an tabo batun muhimmancin tabbatar da adalci da daidaito, yayin da ake gudanar da sauye sauye ga ayyukan kwamitin MDD.

Yayin zaman na jiya, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya gabatar da matsayin Sin, yana mai cewa, karkashin babbar manufar ayyukan kwamitin na tsaro, Sin na fatan za a inganta jagoranci, da aiki bisa kwarewa, kuma ta hanyar aiwatar da manyan sauye sauye, da aiki yadda ya kamata, kwamitin zai kai ga sauke nauyin da aka dora masa bisa dokokin MDD. Ya ce daukacin mambobin kwamitin na fatan ganin an ci gaba da bunkasa ayyuka bisa kwarewa, da samar da karin wakilci, da daidaito da aiki bisa salon dimokaradiyya.

Zhang Jun, ya kuma jaddada bukatar tabbatar da dukkanin kasashen duniya sun ci gajiya daga sauye sauyen. Ya ce MDD na da mambobi 193, kuma kamata ya yi dukkanin su manya da kanana, masu karfi da raunana, masu wadata da matalauta, su ci gajiya daga sauye sauyen da ake fatan yiwa kwamitin na tsaron MDD.

Jami’in ya ce, bai dace sauye sauyen su amfani wasu kasashe kalilan ba. Domin a halin yanzu, akwai rashin daidaito a yanayin moriyar da kasashe masu ci gaba da masu tasowa ke ci daga ayyukan kwamitin.

Zhang Jun ya ce, ya kamata sauye sauyen su magance wasu matsaloli masu nasaba da karfin wakilci da kasashe masu ci gaba ke da shi a kwamitin sama da na takwarorin su masu tasowa, ya kuma ba da damar kara kyautata wakilcin kasashe masu tasowa, da gyara kurakuran rashin adalci da al’ummun Afirka suka fuskanta a tarihi, da baiwa nahiyoyin Afirka, da Asiya, da Latin Amurka, da kasashen Larabawa, da kasashen kananan tsibirai, da sauran kanana da matsakaitan kasashe, damar taka muhimmiyar rawa a kwamitin na tsaron MDD. (Saminu Alhassan)