logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta bi hanyar da ta dace don inganta hulda da Sin

2021-11-16 21:46:01 CRI

Ya kamata Amurka ta bi hanyar da ta dace don inganta hulda da Sin_fororder_amurka

Yau da safe ne agogon Beijing, yayin wata ganawa ta kafar bidiyo tsakanin Sin da Amurka da ta ja hankalin duniya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, abu mafi muhimmanci a dangantakar kasa da kasa cikin shekaru 50 masu zuwa shi ne, wajibi ne kasashen Sin da Amurka su samar da hanyar da ta dace don daidaitawa a tsakaninsu.

Wannan ita ce ganawar bidiyo ta farko da shugabannin biyu suka gudanar, tun bayan zantawa ta wayar tarho sau biyu da shugabannin kasashen biyu suka yi a wannan shekara, inda suka yi magana kan dabaru, gaba daya, da muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban dangantakar Sin da Amurka, da kuma muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Shugabannin kasashen biyu sun amince cewa, ganawar ta kasance bisa gaskiya, mai inganci, ta kuma samar da sakamako mai kyau, wanda za ta taimaka wajen kara fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu, da kuma aikewa da sako mai karfi ga kasar Sin, da Amurka da ma duniya baki daya.(Ibrahim)