logo

HAUSA

Yan bindiga sun kashe mutane 15 a arewa maso yammacin Najeriya

2021-11-16 10:36:30 CRI

Yan bindiga sun kashe mutane 15 a arewa maso yammacin Najeriya_fororder_211116-Ahmad 1

A kalla mutane 15 ’yan bindiga dauke da makamai suka kashe a wani hari da suka kai wasu kauyuka a kananan hukumomi biyu na jihar Sokoto dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda gwamnan jihar ya tabbatar da harin.

Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya bayyanawa ’yan majalisun dokokin jihar da manema labarai a birnin Sokoto cewa, harin ya faru ne a daren Lahadi har zuwa wayewar garin Litinin a kananan hukumomin Illela da Goronyo.

Tambuwal ya mika sakon ta’aziyya ga al’ummun kananan hukumomin Illela da Goronyo, inda aka samu hasarar rayukan mutane 12 a Illela, yayin aka rasa rayukan mutane 3 a karamar hukumar Goronyo, sakamakon harin da ’yan bindigar suka kaddamar. (Ahmad)