logo

HAUSA

Xi: Idan neman ‘yancin kan Taiwan" ya keta iyakan da aka shata, dole ne a dauki tsauraran matakai

2021-11-16 19:01:02 CRI

Xi: Idan neman ‘yancin kan Taiwan" ya tunzura jama’a ko ya keta iyakan da aka shata, dole ne a dauki tsauraran matakai_fororder_xi

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana matsayinsa bisa ka'ida game da batun Taiwan, yayin ganawarsa ta kafar bidiyo da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden, inda ya jaddada aniyarsa ta yin kokarin sake hadewa da yankin cikin lumana bisa gaskiya da himma, amma idan ’yan aware masu neman ‘yancin kan Taiwan suka tunzura jama’a, ko suka zarce layin da aka shata, dole ne a dauki tsauraran matakai.

Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin ba ta da niyyar bunkasa tafarkinta a duk fadin duniya, kuma a ko da yaushe, tana karfafa gwiwar dukkan kasashe da su zabi hanyar ci gaba da ta dace da yanayin kasarsu. Ya ce yana fatan Amurka za ta aiwatar da matsayin da ta furta na rashin amfani da wani "sabon yakin cacar baka".(Ibrahim)