logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron jama'ar Sin da Afirka karo na 6

2021-11-15 18:59:59 CRI

Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron jama'ar Sin da Afirka karo na 6_fororder_sin da afirka

A yau ne, aka gudanar da taron jama'ar Sin da Afirka karo na 6 a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga dandalin.

Xi Jinping ya jaddada cewa, duniya a yau wani zamani ne na babban ci gaba, har ma wani zamani ne da ake samu babban canji. Yayin da ake fuskantar sabbin damammaki da kalubale, Sin da Afirka suna bukatar juna fiye da kowane lokaci, wajen kiyaye da inganta dabi'un zaman lafiya, da ci gaba, da tabbatar da adalci, da dimokuradiyya, da 'yancin dukkan bil'adama, da karfafa hadin kai da hadin gwiwa, da sa kaimi ga wadata da ci gaba da kuma yi aikin tare don gina makomar bil'adama.(Ibrahim)