logo

HAUSA

Bai kamata Amurka ta sake baiwa duniya kunya a wannan karo ba

2021-11-15 19:51:12 CRI

Bai kamata Amurka ta sake baiwa duniya kunya a wannan karo ba_fororder_yanayi

A yammacin ranar 13 ga wata ne, babban taro na 26 na bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD (COP26) da aka gudanar a birnin Glasgow na kasar Birtaniya, ya cimma daftarin kuduri tare da cimma matsaya kan aiwatar da ka'idojin yarjejeniyar Paris.

A matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan kalamai da ayyukan da suka shafi tinkarar sauyin yanayi. A matsakaicin matsayi, sabon yankin da kasar Sin take shuka bishiyoyi ya kai kusan hekta 12,000 a kowace rana, kuma matsakaicin sabbin karfin shigar da wutar lantarki a kullum, ya kai kilowatts 90,000. A saboda haka ne, firaministan Birtaniya Johnson ya nuna godiyarsa ga kasar Sin a bikin bude taron.

Sai dai kuma, har yanzu kasashen duniya na nuna damuwa game da karfin Amurka na iya daukar mataki. Wasu manazarta na ganin cewa, rashin daidaiton da Amurka ke da shi, shi ne babban abin da ke faruwa a hadin gwiwar sauyin yanayi a duniya. Yanzu, akwai bukatar Amurka ta cika alkawuran da ta dauka. (Ibrahim)