logo

HAUSA

Syria ta karbi sabon kashin riga kafin COVID-19 da kasar Sin ta samar

2021-11-15 10:22:07 CRI

Syria ta karbi sabon kashin riga kafin COVID-19 da kasar Sin ta samar_fororder_5d6034a85edf8db1728c66e043b6b15d574e7436

Ma’aikatar lafiya ta kasar Syria, ta karbi wani sabon kaso na alluran riga kafin COVID-19 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin a jiya Lahadi.

Ministan lafiya na kasar Hasan al-Ghabash da jakadan kasar Sin da ke kasar Feng Biao ne suka rattaba hannu kan takardar karbar alluran a Damascus, babban birnin kasar, inda jami’an biyu suka yabawa abotar dake tsakanin kasashensu.

Hasan Ghabash ya bayyana godiya ga kasar Sin da ta samarwa Syria kaso mai yawa na alluran riga kafi domin taimakawa kasar yaki da annobar COVID-19 da kuma ci gaba da yi wa al’ummarta riga kafin.

Ya kara da cewa, alluran kasar Sin sun tabbatar da ingancinsu wajen dakile cutar COVID-19, yana mai cewa sun isa a lokaci mafi dacewa, inda za su taimakawa shirin kasar na yi wa al’umma riga kafi.

A cewarsa, hakika kasar Sin bata yi kasa a gwiwa ba, wajen samar da tallafin lafiya da rigakafi domin taimakawa ma’aikatar lafiya ta Syria sauke nauyin dake wuyanta a wannan lokaci na kalubale.

A nasa bangare, jakadan kasar Sin Feng Biao, ya yi fatan tallafin riga kafin zai taimakawa Syria shawo kan kalubalen da annobar ta haifar.

Ya ce kasar Sin ta aike da kaso da dama na riga kafin COVID-19 ga Syria da ma nau’ika daban daban na kayayyakin kiwon lafiya, domin taimakawa kasar a lokacin da ake fama da annoba. (Fa’iza Mustapha)