logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da zargin kungiyar GATE

2021-11-15 11:02:45 CRI

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da zargin kungiyar GATE_fororder_784

Ministan ma’aikatar al’adu da watsa labarai na tarayyar Najeriya Lai Mohammed, ya ce gwamnatin kasar ta yi tir da wani zargi da wata kungiya mai zaman kan ta ta Amurka ta yiwa Najeriya, cewa wai wasu jami’an kasar ne ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci. Lai Mohammed ya ce kalaman kungiyar Global Advocates for Terrorism Eradication, ko (GATE) a takaice, sun sabawa hankali, kuma wani yunkuri ne na kawar da hankalin al’umma daga hakikanin gaskiya.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, ministan ya ce kungiyar ta GATE na fatan karya lagon kwazon da gwamnatin kasar mai ci ke yi na yaki da ayyukan ta’adanci, da ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran su.

Mohammed ya ce, bai kamata a dauki batun GATE da wani muhimmnaci ba, duba da rudu da rashin sanin ya kamata dake cike da bayanan, wadanda kungiyar ta ce ta samo su daga wani tsohon jami’in leken asiri na rundunar sojin ruwan Najeriyar.

Wasu rahotanni sun ce kungiyar GATE, ta gabatar da korafi ga ofishin sakataren wajen Amurka, inda ta bukaci gwamnatin Amurka da ta ayyana wasu jami’an Najeriya a matsayin masu tallafawa ta’addanci. Kungiya ta ce shaidu na zahiri sun nuna cewa, akwai sa hannun gwamnati a matsalolin ta’addanci dake addabar kasar.   (Saminu)