logo

HAUSA

‘Yan sandan yaki da ta’addanci sun killace wani wuri da aka samu fashewa a Liverpool

2021-11-15 09:41:46 CRI

‘Yan sandan yaki da ta’addanci sun killace wani wuri da aka samu fashewa a Liverpool_fororder_500fd9f9d72a605988bb5a6881c05892023bba13

Rundunar ‘yan sandan yaki da ta’addanci ta Birtaniya, ta ce ta killace wani wuri, bayan da wani abu ya tarwatse cikin wata motar tasi dake kusa da wani asibitin birnin Liverpool, lamarin da ya haddasa rasuwar mutum guda, tare da jikkata wani mutumin na daban. Ba a dai ayyana wannan lamari a matsayin harin ta’addanci ba.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta bayyana cewa, fashewar ta auku ne da misalin karfe 11 na safiyar jiya Lahadi, kusa da asibitin mata dake tsakiyar birnin Liverpool. An kuma ga wuta da hayaki na tashi daga motar da ta yi bindiga.

‘Yan sanda yaki da ta’addanci da hadin gwiwar na Merseyside, sun dukufa wajen gudanar da bincike game da lamari, ko da yake sun bayyana cewa, mai yiwuwa a dan dau lokaci kafin tabbatar da hakikakin abun da ya haddasa fashewar.

A wani ci gaban kuma, kafar watsa labarai ta Sky News ta rawaito cewa, ‘yan sanda sun damke wasu mutane 3 bayan aukuwar wannan fashewa.   (Saminu)