logo

HAUSA

Adadin mutanen da suka samu aiki bayan kubuta daga talauci a Sin ya kai miliyan 31.03

2021-11-14 16:45:14 CRI

Sabbin alkaluman da ma’aikatar kwadago da kyautata zamantakewar al’umma ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Satumban da ya gabata, gaba daya adadin mutanen da suka samu guraben aikin yi bayan da suka kubuta daga kangin talauci ya kai miliyan 31.02 a fadin kasar, wato an kammala aikin da aka tsara na bana tun kafin cikar wa’adinsa.

Jami’in hukumar samar da ayyukan yi na ma’aikatar ya bayyana cewa, tun daga farkon bana, yanayin samun aikin yi a kasar Sin yana da inganci, har ya zarta hasashen da aka yi, wato tsakanin watan farko zuwa watan Satumba, karin mutane miliyan 10.45 sun samu guraben aikin yi a birane da garuruwan kasar, adadin da ya karu da miliyan 1.47 wato kaso 16 bisa dari idan an kwatanta da makamancin lokacin bara.

An lura cewa, a cikin rubu’i na uku na bana, sana’o’in ba da hidima sun kyautata a fadin kasar Sin, a sakamakon haka, an samar da karin sabbin guraben aikin yi.(Jamila)