logo

HAUSA

An rufe taron COP26 tare da cimma sabuwar matsaya kan sauyin yanayi

2021-11-14 16:30:07 CMG

An rufe taron COP26 tare da cimma sabuwar matsaya kan sauyin yanayi_fororder_1114-COP26-Ahmad

Taron kolin sauyin yanayi na MDD ya kammala a ranar Asabar bayan tsawaita wa’adin taron da kwana guda, inda mahalarta taron suka amince da sabuwar yarjejeniyar kasa da kasa game da yadda za a tinkari batun magance matsalolin sauyin yanayi.

Kimanin mahalartan kasashen duniya 200 ne suka amince da yarjejeniyar Glasgow, a karshen taron kolin sauyin yanayin na MDD karo na 26 wato COP26.

An samu nasarori masu karfafa gwiwa. Daga karshe an cimma matsaya kan yarjejeniyar Paris mai lamba ta 6, wacce ke shafar batun matakan daidaita kasuwannin samar da makamashi mai gurbata muhalli, lamarin da ya samar da kyakkyawan tsari na aiwatar da yarjejeniyar Paris na rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli ta hanyar daidai kasuwannin samar da makamashin mai gurbata muhalli.

Mahalartan sun kuma cimma matsaya game da rage amfani da makamashin kwal, a matsayin hanya mafi girma na samar da makamashi dake fitar da hayaki mai gurbata muhalli yayin da ake amfani da shi wajen samar da lantarki.(Ahmad)

Ahmad