logo

HAUSA

Jakadan Sin a Amurka ya bukaci Amurka da ta nace kan manufar kasar Sin daya tak a duniya

2021-11-14 16:24:26 CRI

Jiya Asabar 13 ga wata, jakadan Sin dake kasar Amurka Qin Gang, ya bukaci Amurkar da ta nace kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma ta cika alkawarin da ta yiwa kasar Sin kan batun Taiwan, ta yadda za a gujewa sabanin da zai iya faruwa tsakanin kasashen biyu wato Sin da Amurka sakamkon batun.

An kira taron shekara shekara na shekarar 2021 na hadaddiyar kungiyar ingiza dungulewar kasar Sin cikin lumana ta Amurka a birnin San Francisco, inda jakada Qin Gang, ya taya murna ta kafar bidiyo, kuma ya gabatar da jawabi cewa, cikin dogon lokaci kungiyar ta taka babbar rawa wajen ingiza dunkulewar kasar Sin cikin lumana.

Qin Gang, ya yi nuni da cewa, a halin yanzu matakan da jam’iyyar DPP wato jam’iyyar ci gaban demokuradiyya ta hukumar Taiwan ta dauka, suna jefa al’ummun yankin Taiwan cikin mawuyacin hali na “yancin kan Taiwan”, matakan da suka gurgunta babbar moriyar al’ummun Sinawa da ‘yan uwa Sinawa dake rayuwa a yankin Taiwan, haka kuma suna lalata yanayin kwanciyar hankali a zirin Taiwan.(Jamila)