logo

HAUSA

Kasar Sin na goyon bayan samar da hanya mai dorewa ta samar da kudade ga rundunar kawance ta yankin Sahel

2021-11-13 16:16:38 CRI

Kasar Sin na goyon bayan samar da hanya mai dorewa ta samar da kudade ga rundunar kawance ta yankin Sahel_fororder_QQ图片20211113152312

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Dai Bing, ya ce kasar Sin na goyon bayan kokarin da ake na samar da kudade ga rundunar kawance ta yankin Sahel wato G5, wadda ke da alhakin yaki da ta’addanci.

Ya ce kasar Sin na bada muhimmianci ga damuwar kasashen yankin game da batutuwan kudi, kuma tana goyon bayan rundunar kawancen wajen samun tallafin kudi mai dorewa.

Ya kara da cewa, Sin na goyon bayan kokarin da ake na samar da mafita ga dukkan matsalolin bangarori masu rikici nan bada jimawa ba, wadda kuma za ta dace da yanayin yankin da cimma bukatun rundunar kawancen, haka kuma za ta yi la’akari da bukatun masu ruwa da tsaki.

Kasashen na Sahel G5 sun hada da Burkina Faso da Mali da Chadi da Mauritania da Niger.

Bugu da kari, Dai Bing ya ce a shekarun baya-bayan nan, kasashen 5 na Sahel, sun karfafa kansu ta hanyar zurfafa hadin gwiwar yaki da ta’addanci da kaddamar da jerin ayyukan yaki da ta’addanci, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kawar da mummunan tasirin ta’addanci da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da tsaro. Yana mai cewa, Sin na yabawa kasashen na Sahel. (Fa’iza Mustapha)