logo

HAUSA

Rundunar sojin Sudan ta gabatar da dokar kafa gwamnatin rikon kwarya

2021-11-12 10:50:24 CRI

Rundunar sojin Sudan ta gabatar da dokar kafa gwamnatin rikon kwarya_fororder_1112-Faiza2

Babban kwandan rundunar sojin Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, ya gabatar da wata dokar kafa gwamnatin rikon kwarya a jiya.

Dokar ta ayyana Al-Burhan a matsayin shugaban gwamnatin rikon da kuma Janar Mohamed Hamdan Daqlu a matsayin mataimakin shugaba, da sauran wasu mutane 11 a matsayin mambobi.

Bugu da kari, dokar ta jinkirta nada wakilin gabashin Sudan a majalisar, har zuwa lokacin da za a kammala tattaunawa game da batun. (Fa’iza Mustapha)