logo

HAUSA

Sin: ’Yan siyasar Amurka da ke rawar kafa kan batun Taiwan suna wasa da wuta

2021-11-12 10:44:18 CRI

Sin: ’Yan siyasar Amurka da ke rawar kafa kan batun Taiwan suna wasa da wuta_fororder_1112-Ibrahim2-Sin da Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya bayyana a wata hira da aka yi da shi a kwanakin baya cewa, Amurka na da kudurin tabbatar da cewa, yankin Taiwan zai iya kare kansa. Sai dai kuma Anthony Blinken ya bayyana a wani taron manyan jami’an kasashen Sin da Amurka da aka gudanar a karshen watan da ya gabata, cewa  "Amurka za ta ci gaba da bin manufar Sin daya tak a duniya". Don haka, ta yaya irin wannan kwan-gaba-kwan baya ya yi kama da babban jami'in diflomasiyyar Amurka?

Ya kamata Blinken ya fahimci cewa, akwai kasashe 180 a duniya, wadanda suka amince da kuma goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma wannan ita ce yarjejeniya ta gaskiya ta kasa da kasa, suka amince da ita. Dokar dangantakar Taiwan da Amurka da Amurkar ta kirkita, ta saba alkawurran da ta dauka a cikin sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma a tsakaninsu.

A jiya ne, aka fitar da sanarwar cikakken zaman karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, inda ya bayyana karara cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma matsaya kusan iri daya da aka cimma a shekarar 1992, wadda ke adawa da ayyukan ’yan aware dake neman ’yancin kai na Taiwan, da tsoma baki daga waje. Wannan ya nuna a fili irin tsayin daka na kasar Sin, da kuma matsayinta na kare ikon mallakar kasa, da tsaro da moriyar ci gabanta

A halin da ake ciki yanzu, babban yankin kasar Sin, ya amince da jagoranci da himma a dangantakar dake tsakaninsa da zirin Taiwan, kuma batun sake hadewar kasar Sin, wani yanayi ne na tarihi da ba za a iya jurewa ba. A don haka, kasar Sin tana gargadin bangaren Amurka da kada ya raina kudiri da karfin da jama'ar kasar Sin suke da shi, na kare ikon mallakar kasa da cikakkun yankanansu. Kuma duk wani mataki na kalubalantar manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kokarin dakile kokarin sake dinkuwar kasar Sin baki daya, to hakika ba zai taba yin nasara ba. (Ibrahim Yaya)