logo

HAUSA

Cikakken zaman taro na shida na kwamitin tsakiya na JKS ya zartas da kuduri mai taken tarihi karo na uku a tarihin jam'iyyar na shekaru dari

2021-11-12 10:06:26 CRI

Cikakken zaman taro na shida na kwamitin tsakiya na JKS ya zartas da kuduri mai taken tarihi karo na uku a tarihin jam'iyyar na shekaru dari_fororder_1112-Ibrahim1-hoto1

A jiya Alhamis ne, aka kammala cikakken zaman taro karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19 a nan birnin Beijing. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, ya gabatar da muhimmin jawabi a zaman taron. Taron dai ya yi nazari tare da zartas da wasu muhimman takardu na siyasa guda biyu: kudurin kwamitin tsakiya na JKS kan manyan nasarori da gogewar da jam'iyyar ta samu a cikin shekaru 100 na gwagwarmayar da jam'iyyar ta yi, da kuma kuduri kan babban taron jam'iyyar na kasa karo na 20.

Taron ya yi nuni da cewa, tun bayan kafuwar JKS a shekarar 1921, ta yi nasarar hada kai tare da jagorantar al'ummar Sinawa na dukkan kabilun kasar Sin, wajen fafutukar neman 'yancin kai da 'yantar da kasa, da samun wadata da jin dadi, tare da rubuta al’amura masu ban al’ajabi a cikin dubban shekaru na tarihin kasar Sin.

Cikakken zaman taro na shida na kwamitin tsakiya na JKS ya zartas da kuduri mai taken tarihi karo na uku a tarihin jam'iyyar na shekaru dari_fororder_1112-Ibrahim1-hoto2

Yayin da ake takaita manyan nasarori da gogewar tarihi na yin gyare-gyare, da bude kofa da zamanantar da tsarin gurguzu a cikin sabon zamani, taron ya nuna cewa, yin kwaskwarima da bude kofa ga waje, na da matukar muhimmanci wajen tantance makomar kasar Sin ta zamani da makomarta tafarkin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, wadda ke zama hanya madaidaiciya ta jagorantar ci gaban kasar Sin da samun wadata.

Cikakken zaman taro na shida na kwamitin tsakiya na JKS ya zartas da kuduri mai taken tarihi karo na uku a tarihin jam'iyyar na shekaru dari_fororder_1112-Ibrahim1-hoto3

Taron ya yi nuni da cewa, tun bayan babban taron JKS karo na 18, tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, ya shiga wani sabon zamani. Kwamitin tsakiya na JKS da Xi Jinping ke jagoranta, ya yayata nasarorin da aka samu a tarihi da kuma sauye-sauye a harkokin jam'iyyar da kuma kasar Sin baki daya. (Ibrahim)