Yariniyar dake wasan Kongfu
2021-11-12 19:58:03 cri
Wannan ne yadda Ma Liye da kakanta mai shekaru 84 a duniya ke wasan Kongfu na Bamenquan. Tun lokacin da shekarun ta na haihuwa suka kai 5 kawai, sai Ma Liye ta soma koyon wasan Kongfu tare da kakanta, a cikin shekaru 10 da wani abu da suka wuce, ta halarci gasanni na cikin gida da na ketare har sau sama da 100, ya zuwa yanzu ta riga ta samu lambobin zinari sama da 80 da na azurfa sama da 50.