logo

HAUSA

Sharhi: Makomar dan Adam daya ce

2021-11-12 22:11:16 CRI

Sharhi: Makomar dan Adam daya ce_fororder_微信图片_20211112214112

Kwanan nan, na ji wani labarin da ya faranta mini rai matuka, wanda ke cewa harkokin yawon shakatawa na farfadowa a birnin Victoria Falls na kasar Zimbabwe, bayan tsawon watanni 18 fannin yana fama da kaka-nika-yi. Wani shirin

bidiyon da kafar talabijin ta ZTN ta watsa, ya yi nuni da cewa, hakan ya faru ne sakamakon shawarar da gwamnatin kasar ta yanke, ta yiwa al’ummar kasar rigakafi bisa gudummawar da kasar Sin ta samar.

Harkokin yawon shakatawa na daga fannonin da suka fi fuskantar illolin da annobar Covid-19 ke haifarwa. Tun bayan barkewar annobar a bara, harkokin sun kusan tsayawa cik a birnin na Victoria Falls, birnin da akasarin mazaunansa ke dogara ga harkokin yawon shakatawa wajen samun kudin shiga. Amma yanayin ya fara kyautatuwa a karshen watan Maris na wannan shekara, a sabili da yadda aka fara yi wa al’ummar birnin rigakafin da kasar Sin ta samar.

Ya zuwa karshen watan Afrilu, aka yi wa kimanin kaso 77% na mazauna birnin rigakafi, matakin da ya sa birnin ya zama na farko a kudancin Afirka, da daukacin al’ummarsa suka samu kariya daga cutar, kuma birnin ya zama daya daga cikin wuraren yawon shakatawa da suka fi tsaron lafiya a duniya. Bisa ga shirin bidiyo, wata bakuwa da ke yawon bude ido a birnin ta ce, dalilin da ya sa ta zabi birnin shi ne, don ya fi tsaron kiwon lafiya a yankin.

Tun bayan barkewar annobar, a yayin da kasashe masu ci gaba ke kokarin tattare alluran rigakafi, kasar Sin a nata bangaren ta samar da rigakafi masu yawa ga kasashe masu tasowa, don daidaita matsalar da suke fuskanta. Tuni kasar ta samar da rigakafi sama da biliyan 1.7 ga kasashe da kungiyoyin duniya sama da 100, matakin da ya sa ta zama kasar da ta fi yawan samar da rigakafi a duniya.

Sharhi: Makomar dan Adam daya ce_fororder_微信图片_20211112214006

Amma a hakika, kasancewarta kasar da ke da al’umma kimanin biliyan 1.4, kasar Sin ita kanta tana fuskantar kalubale ta fannin kandagarkin cutar. To, ko me ya sa kasar take samar da rigakafi masu yawa haka ga sauran kasashen duniya?

Ko shakka ba bu dalili shi ne, jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ko (JKS), ta kasance jam’iyyar da ke rungumar duniya baki daya, wadda ta san cewa, makomarta hade take da ta sauran kasashen duniya. A gun taron shugabannin JKS da na sauran jam’iyyun siyasa da ya gudana a watan Yulin da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi nuni da cewa, “’Yan Adam a dunkule suke, kuma duniya daya ce gare mu. A yayin da muke fuskantar kalubale na bai daya, ba wanda zai iya tsira shi kadai. Ya zama dole ‘yan Adam su hada kawunansu.”

To, wannan kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Sin take tsayawa kan hadin gwiwar samun moriyar juna, da bude kofarta ga ketare, da kuma cudanyar kasa da kasa, a yayin da kuma take kin jinin nuna kiyayya ga juna, da kariyar ciniki da ma ra’ayi na kashin kai.

Sharhi: Makomar dan Adam daya ce_fororder_微信图片_20211112214048

 

A gun bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin(CIIE) karo na hudu da ya kammala ba da jimawa ba, an tallata tare da sayar da ‘ya’yan itacen pine, har ton dubu 260 da aka shigo da shi daga kasar Afghanistan cikin sa’o’i biyu kacal. An ce, bana an samu girbi mai armashi na ‘ya’yan itacen pine a Afghanistan, sai dai kuma an gamu da matsalar sayar da su sakamakon annobar cutar COVID-19, da ma halin da ake ciki a kasar. Don haka, kasar Sin ta shigo da kayan kasuwar kasar Sin, don taimakawa ga daidaita matsalar da manoman Afghanistan ke fuskanta. Abin lura shi ne, bikin CIIE da aka kaddamar a shekarar 2018 ya kasance biki irinsa na farko a duniya da ke baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su. A yayin da ake kara fuskantar kariyar ciniki a duniya, ita kuwa kasar Sin na kara bude kasuwarta, matakin da ya shaida yadda kasar Sin ke rungumar kasashen duniya baki daya.

Bana jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin take cika shekaru 100 da kafuwa. Kasancewarta jam’iyyar da ke jagorantar al’ummar Sinawa biliyan 1.4 wajen samun ci gaban a zo a gani, shin “ko me ya sa jam’iyyar ta iya kaiwa ga wannan nasara” ta dade da zama babbar tambaya. Daga ranar 8 zuwa 11 ga wata, kwamitin kolin jam’iyyar ya gudanar da babban taronta, kuma kudurin da taron ya zartas ya waiwayi tarihin jam’iyyar, tare da takaita wasu fasahohinta 10, da ke sa ta cimma nasarar hakan, wadanda suka ba da amsa ga tambayar, kuma “rungumar kasashen duniya” na daya daga cikin fasahohin. 

Ci gaban kasar Sin ba ya iya rabuwa da duniya, haka kuma kasar Sin na kara samar da gudummawarta ga duniya bisa ci gaban da take samu. A ci gaban kokarinta, kasar Sin za ta ci gaba da rungumar kasashen duniya, don tabbatar da ci gaban duniya tare. (Lubabatu)