logo

HAUSA

Taron kwamitin tsakiya na JKS ya nuna wayewar kan jam’iyyar ta fuskar siyasa da kuma jajircewarta

2021-11-12 15:29:18 CRI

Taron kwamitin tsakiya na JKS ya nuna wayewar kan jam’iyyar ta fuskar siyasa da kuma jajircewarta_fororder_1112-Faiza3

An bayyana taro na 6 na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19 da aka kammala a baya-bayan nan, a matsayin wanda ya nuna wayewar kan da jam’iyyar ke da shi a fannin siyasa da jajircewarta da kuma kwarin gwiwarta.

Mataimakin babban daraktan sashen yada labarai na kwamitin tsakiya na JKS, Wang Xiaohui ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya ce yayin da jam’iyyar ke cika shekaru 100 da kafuwa, nazarin manyan nasarori da tarihin jam’iyyar cikin wadancan shekaru da taron ya yi, muhimmin mataki ne da jam’iyyar ta dauka.

A cewrasa, kudurin da taron ya amince da shi, ya bayyana dalilin da ya sa ta samu nasarori a baya, da kuma yadda za ta ci gaba da samun nasara nan gaba. (Fa’iza Mustapha)