logo

HAUSA

Karancin Matakan Da Gwamnatin Amurka Ke Dauka Ya Haddasa Karuwar Hare-haren Bindiga A Kasar

2021-11-11 15:02:58 CRI

Karancin Matakan Da Gwamnatin Amurka Ke Dauka Ya Haddasa Karuwar Hare-haren Bindiga A Kasar_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_q_70,c_zoom,w_640_images_20180325_e68899ffb11148968bce4adc1321faf4.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Daga Amina Xu

Abokaina, hare-haren bindiga ya kan faru a Amurka. Abin bakin ciki shi ne a ran 6 ga wata, an yi musanyar wuta a wata hanyar mota dake jihar California, lamarin da ya halaka wani karamin yaro da shekarunsa bai kai 2 ba. Shafin yanar gizo na GVA mai kidaya hare-haren bindiga ya ba da rahoto cewa, ya zuwa ran 8 ga watan nan, yawan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a kalla 4 a shekarar 2021 ya kai 611, wato ya kan faru sau biyu a ko wace rana. Ba shakka, al’ummar Amurka na fuskantar hare-haren karfin tuwo, kuma dalilin da ya sa hakan shi ne yadda al’ummar kasar ke fama da matsalolin cutar COVID-19 da hauhawar farashi da nuna bambancin launin fata.

Yanzu cutar na kan ganiyarta a Amurka saboda rashin daukar matakan da suke dacewa masu inganci wajen kandagarki, da karancin karfin farfadowar tattalin arziki da karuwar rashin aikin yi da kuma rikicin al’umma dake kara tsananta da sauransu sun yi sanadin karuwar nuna karfin tuwo dake da alaka da bindiga.

A wani bangare kuma, al’ummar Amurka na kara fuskantar rashin tabbas saboda ganin ba a iya hana yaduwar cutar Covid-19 a kasar, abin da ya kara tsanantar da hare-haren bindiga da kasar ke fuskanta. A wani bangare kuwa, al’umma na damuwa da karuwar hare-haren bindiga sosai, hakan ya sa karin mutane ke sayen bindiga don kare kansu. Kwanan baya, wasu kafofin yada labarai na Amurka sun ba da labari cewa, wasu kantunan sayar da makamai na karancin harsashi, har wasu sun kayyade yawan bindiga da za a saya. Wani mai amfani da yanar gizo ya nuna cewa, al’ummar Amurka ba su amince cewa gwamnatin kasar za ta iya kare su a irin wannan hali ba. Gwamnatin Amurka ta kan fuskantar rikicin samun amincewa a fannin tabbatar da tsaron al’umma.

Ko da yake wasu jama’ar Amurka suna ganin cewa, akwai wajibcin hana yaduwar bindiga, amma jam’iyyar RP mai goyon bayan mallakar bindiga da jam’iyyar DP mai ra’ayin kayyade yawan bindiga suna adawa da juna kan wannan batu saboda yana da alaka da moriyarsu, da kuma rikicin al’umma musamman ma ra’ayin bambancin launin fata da dai sauransu, dukkan abubuwa da ya sa gwamnatin Amurka ba ta iya warware matsalar hare-haren bindiga a siyasance ba.

‘Yancin rike bindiga da al’ummar Amurka ke da shi ba ainihin ‘yanci ba, sabo da zai haddasa rasuwar fararen hula, abin matukar bakin ciki ne. A idanun ‘yan siyasar kasar, hasarorin rayukan mutane ciki hadda kananan yara ba abu ne mai muhimmanci ba, hakan ya sa irin wannan abu zai kara faruwa nan gaba. (Amina Xu)