logo

HAUSA

Sin Ta Zamo Garkuwa Ga Raya Hada Hadar Cinikayyar Kasa Da Kasa Karkashin Kungiyar WTO

2021-11-11 17:04:55 CRI

Sin Ta Zamo Garkuwa Ga Raya Hada Hadar Cinikayyar Kasa Da Kasa Karkashin Kungiyar WTO_fororder_WTO

Jiya 10 ga watan Nuwamba rana ce ta cika shekaru 20 da kungiyar cinikayya ta duniya WTO ta amince da kasar Sin a matsayin mambar kungiyar. Sannan a ranar 11 ga watan Disambar shekarar 2001 ne ministan kasuwancin kasar ta Sin na wancan lokaci, ya rattaba hannu kan takardun amincewa da hakan a hukumance a birnin Doha na kasar Qatar.

Tun bayan wannan lokaci ne kuma, Sin ke ci gaba da taka rawar gani a fannonin ayyukan kungiyar, musamman ma bangaren yayata manufar bude kofofin kasuwanni, da kare ka’idojin kungiyar WTO, da ingiza manufar cudanyar sassa daban daban, tare da kalubalantar baiwa kasuwa kariya, da sanya shinge cinikayya.

Duk da irin wadannan matakai da kyawawan manufofi da kasar Sin ke aiwatarwa cikin shekaru 20 da suka gabata, akwai wasu sassa na kasashen yammacin duniya dake sukar ta, musamman ma Amurka, wadda ta jima tana yayata cewa, wai Sin din na yiwa ka’idojin cinikayyar kasa da kasa karan tsaye.

To sai dai kuma masharhanta da dama, ciki har da na kasashen yamman su kan su, sun shaida yadda kasar Sin ke cika dukkanin alkawura da ta dauka, take kuma martaba dukkanin dokokin cinikayyar kasa da kasa karkashin lemar kungiyar ta WTO. Lamarin da ya sa da dama daga masu fashin baki suka amince cewa, Sin ta zama wata garkuwa dake baiwa dokokin cinikayyar duniya kariya.

Wani abun lura ma a nan shi ne, a duk lokacin da Amurka ta furta zargin cewa Sin na kin bin wasu dokoki na cinikayyar kasa da kasa, za a tarar cewa, irin wadannan dokoki ba komai a cikin su illa tsare tsaren Amurka na kashin kan ta, da take nufin tirsasawa sauran kasashen duniya su bi.

Kaza lika, a duk tsawon wadannan shekaru 20 da Sin ta yi cikin kungiyar WTO, an ga yadda a zahiri ta taimakawa kungiyar wajen sauya dokokin gudanar da ayyuka, da tallafawa ayyukan warware rikici, yayin da a nata bangare Amurka, ke ta kokarin rura wutar cacar baka, da takara mai hadari.

Bugu da kari, a wannan gaba da tattalin arzikin duniya ke fama da yanayi na rashin tabbas, Sin na ci gaba da biyayya ga ka’idojin WTO, tana sauke nauyin dake kan ta a matsayin kasa mai karfin tattalin arziki. Don haka, fatan shi ne ita ma Amurka, da sauran kasashen yamma masu wadata za ta bi sahu, na sauke nauyin dake wuyan su bisa jagorancin WTO, ta yadda duniya baki daya za ta ci gajiyar ayyukan kungiyar yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)