logo

HAUSA

Sin na kokarin ciyar da yankin Asiya da tekun Pasifik gaba

2021-11-11 19:55:31 CRI

Sin na kokarin ciyar da yankin Asiya da tekun Pasifik gaba_fororder_APEC

Yankin Asiya da tekun Pasifik, yana taka babbar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin duniya, amma yanzu yana fama da wahalhalun da annobar COVID-19, da dalilan siyasa suka haifar. Ko yankin zai ci gaba da bunkasa bisa fiffikonsa yadda ya kamata? Yau Alhamis 11 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da amsa mai tabbaci yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a taron shugabannin masana’antu da kasuwanci na kungiyar APEC, inda ya bayyana cewa, “Duk da cewa yanayin duniya ya yi manyan sauye-sauye, amma fiffikon tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasifik ba zai canja ba.”

A halin yanzu, bunkasuwar yankin Asiya da tekun Pasifik ya gamu da sabbin damammaki da kalubaloli, a don haka shugaba Xi ya yi kira ga sassa daban daban da su hada kai, su yi kokari tare, domin gina kyakkyawar makomar al’ummun yankin Asiya da tekun Pasifik, kuma ya gabatar da shawarwari guda hudu dake kumshe da kandagarkin annobar COVID-19, da nacewa kan manufar bude kofa da hadin gwiwa, da ingiza ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma sa kaimi kan kirkire-kirkire, shawarwari hudun da za su taimaka wajen raya yankin Asiya da tekun Pasifik, haka kuma za su ba da jagoranci kan kiyaye tsarin da yankin ke bukata.

Hadin gwiwa tsakanin kasashen dake yankin Asiya da tekun Pasifik ba wasan siyasa ne da ake yin takararsa ba. Maimakon haka, dandali ne na amfanar juna da ake gudanarwa ba tare da rufa rufa ba. (Jamila)