Kasar Sin za ta hau duniyar wata, tare da kasashen Afirka
2021-11-11 15:08:34 CRI
A kwanakin nan na ji wasu labaru masu alaka da hadin gwiwar kimiyya da fasaha tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, inda wani labari ya nuna cewa, wasu manazarta fasahar aikin gona na kasar Sin, sun samar da wani sabon nau’in shinkafa, wadda za ta iya jure yanayi mai matukar zafi,wadda kuma za a iya shuka ta a wasu wurare masu zafi dake nahiyar Afirka.
Yayin da wani labari na daban ke cewa, an gudanar da dandalin hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin a fannin tsarin tauraron dan adam na lura da harkar sufuri na kasar Sin, da aka yiwa lakabi da “Beidou”, tsarin da zai iya taimakawa kasashen Afirka raya bangaren sufuri. Wadannan kayayyaki na kimiyya da fasaha sun shafi abinci, da zirga-zirga, wadanda suka nuna tasirin hadin kan kasashen Afirka da kasar Sin, a fannin kimiyya da fasaha, da zaman rayuwar jama’ar kasashen Afirka.
Lokacin da suke magana kan hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha, wasu jami’an Najeriya su kan bayyana cewa: “Idan kasar Sin za ta hau duniyar wata, ya dace ta tafi tare da Najeriya”. Wannan magana ta nuna yadda suke da burin hadin gwiwa da kasar Sin don ciyar da kimiyya da fasahar Najeriya gaba. To sai dai kuwa ko Sin na son “hawa duniyar wata” tare da Najeriya?
Amsar da kasar Sin ta bayar ita ce “Ina so”. Saboda shugaban kasar Sin Xi Jinping, yayin da yake halartar taron muhawara na babban taron MDD a watan Satumban bana, ya taba gabatar da wata shawara ta raya duniya, wadda ta shafi yadda kasar Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa da sauran kasashe masu tasowa, don neman samun ci gaba na bai daya. Wannan shawara ta kunshi fannonin dake matukar maida muhimmanci kan moriyar jama’a, da kirkiro sabbin fasahohi don raya tattalin arziki da dai sauransu, wadda ta nuna yadda wata kasa mai tasowa take iya samun ci gaba cikin sauri.
Dalilin da ya sa kasar Sin ta ba da wannan shawara, shi ne ta taba kokarin neman hanyar raya kanta, inda ta fara daga wata kasa mai fama da talauci, daga baya ta zama mai matsakaicin karfi. Ta wannan hanya, kasar Sin ta fahimci ma’anar samun ci gaban fasahohi da na tattalin arziki, game da yadda za a kyautata zaman rayuwar jama’ar wata kasa, da tabbatar da ingantuwar hakkin dan Adam a duniya. Ban da wannan kuma, yadda wasu kasashen dake yammacin duniya suka yi kokarin hana kasar samun ci gaba, shi ma ya sa kasar Sin fahimtar muhimmancin dogaro da kai, a kokarin neman samun sabbin fasahohi, da kawar da rashin adalci a cikin yanayi na samun bambanci sosai tsakanin kasashe masu karfin tattalin arziki da kasashe marasa karfi.
Bisa shawarar raya duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, za mu iya tabbatar da yanayin da za a samu a fannin hadin kan Afirka da Sin a bangaren kimiyya da fasaha:
Da farko, ana gudanar da wannan hadin kai ne don neman ci gaban tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’ar kasashen Afirka. Ta wadannan labaru 2 da na ambata a baya, za a iya ganin yadda hadin gwiwar da ake yi tsakanin Afirka da Sin a fannin kimiyya da fasaha, ta fi dora muhimmanci kan raya masana’antu da aikin gona a kasashen Afirka, inda za a samar da karin guraben aikin yi, da biyan bukatun jama’a na inganta zaman rayuwa.
Na biyu, mika fasahohi, da samun ci gaba tare, za su zama tushen huldar hadin kai tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin ta raya kimiyya da fasaha. Cikin shawarar da kasar Sin ta gabatar, ta riga ta jaddada cewa, bai kamata ba a ci gaba da yin babakere a duniya a fannin kimiyya da fasaha, domin kasashe masu tasowa su ma suna da ikon raya fasahohi na kansu. Saboda haka, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin ba da taimako ga kasashen Afirka, musamman ma a fannin horar da kwararrun ma'aikata.
Na uku, shi ne kasar Sin za ta dora muhimmanci kan daukar hakikanan matakai. Ta wasu ayyukan hadin kai da ake gudanar da su tsakanin masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashen Afirka da na kasar Sin, da yadda Sinawa suke gina wasu manyan gandayen gona na zamani a Mozambique, da dai sauransu, za a iya ganin tunanin kasar Sin na daukar hakikanan matakai don taimakawa kasashen Afirka raya kimiyya da fasaha.
Fatan muke kasashen Afirka su iya yin amfani da damar samun sauyawar yanayi a fannin kimiyya da fasaha, wajen kirkiro sabbin fasahohi, da raya masana’antu, ta yadda za su iya samun ci gaba cikin sauri tare da kasar Sin. (Bello Wang)