logo

HAUSA

Libya ta tattauna da shiyyoyi game da hadin gwiwar magance matsalar yan ci rani

2021-11-11 11:56:26 CRI

Libya ta tattauna da shiyyoyi game da hadin gwiwar magance matsalar yan ci rani_fororder_211111-Libya-Ahmad4

Ministan kwadago na kasar Libya, Ali Abed Al-Reda, ya gana da wakilan shiyyoyin kasashe na duniya don tattauna yadda za a karfafa hadin gwiwa da nufin inganta harkokin ’yan ci rani da magance matsalolinsu.

Mahalarta taron sun kunshi wakilin musamman na kungiyar EU dake Libya, da jami’an diflomasiyyar kasashen Burkina Faso, Chad, Masar, Ghana, Guinea Conakry, Mali, Nijer, Najeriya, Sudan da Tunisia.

Babban jami’in kungiyar kula da bakin haure ta kasa da kasa IOM, dake Libya, Federico Soda, ya bayyana a wajen taron cewa, ingantaccciyar hadin gwiwar kasa da kasa game da ’yan ci rani al’amari ne mai matukar muhimmanci wanda zai kara inganta dabarun tabbatar da lafiya da tsaron ’yan ci rani wadanda ke bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar Libya. Ya ce kamar yadda aka sani, adadin ’yan ci rani 610,000 dake aiki a Libya suna daga cikin babban ginshikin bunkasa kasuwar samar da ’yan kwadago ta kasar Libya. (Ahmad)