logo

HAUSA

Shugaban majalisar koli ta Libya ya bukaci masu kada kuri’a su kauracewa zaben kasar

2021-11-10 10:04:07 CRI

Khaled al-Meshri, shugaban majalisar koli mai bayar da shawara ga batun siyasar kasar Libya, ya yi kira ga masu kada kuri’a su kauracewa zabukan kasar dake tafe.

Al-Meshri ya yi wannan tsokaci ne jiya, yayin ganawarsa da mambobin majalisar da ‘yan majalisar dokoki da jakadu da dama dake Libya.

Ya yi kira ga al’ummar kasar su kauracewa zabukan, tare da gudanar da zanga-zangar lumana a gaban ofishin MDD dake kasar da hukumar zabe.

Har ila yau, ya bayyana adawa da dokokin zaben da majalisar wakilan kasar ta gabatar, yana mai bayyana su a matsayin abun kunya.

Sama da masu kada kuri’a miliyan 2.8 ne ake sa ran za su kada kuri’a domin zaben shugaban kasar a zaben ranar 24 ga watan Disamba, a matsayin wani bangare na dabarun warware rikicin siyasar kasar da MDD ta dauki nauyi.

An dage zabukan ‘yan majalisar dokoki da aka shirya yi rana guda da na shugaban kasa, zuwa watan Janairun 2022. (Fa’iza Mustapha)