logo

HAUSA

Kamfanoni da dama sun bayyana niyyarsu ta sake halartar bikin CIIE a shekara mai zuwa

2021-11-10 21:18:29 CRI

Kamfanoni da dama sun bayyana niyyarsu ta sake halartar bikin CIIE a shekara mai zuwa_fororder_微信图片_20211110202326

Daga ranar 5 zuwa 10 ga watan nan ne, aka gudanar da bikin CIIE karo na 4 a birnin Shanghai na kasar Sin, wato bikin baje-kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin. Rahotannin sun ce, darajar yarjejeniyoyin da aka daddale a wannan karo ta zarce dala biliyan 70.7, kuma akwai kamfanoni da dama da suka bayyana niyyarsu ta sake halartar bikin a shekara mai zuwa.

A cikin yarjejeniyoyi sama da 200 da kamfanonin Sin da kasashen waje fiye da 1000 suka daddale, kasashen dake aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” sun samu yarjejeniyoyi da yawa. Haka kuma, kamfanoni kimanin 90 daga kasashe 33, wadanda ke fama da rashin ci gaba sun halarci bikin a bana, al’amarin da ya shaida cewa, CIIE ya kasance dandali ga kowace kasa don more damammakin ci gaba tare.

Abun lura a nan shi ne, akwai kamfanoni kimanin 200 na kasar Amurka wadanda suka halarci bikin a bana. Hasali ma, kasuwar kasar Sin na jawo hankalin manyan kamfanonin kasa da kasa. Ganin yadda kasuwar kasar Sin ke da girma, da babbar bukatar da ake da ita sakamakon farfadowar tattalin arzikin kasa, da kuma samar da ci gaba mai inganci, kasar Sin ta samarwa duk duniya manyan damammakin kasuwanci, da karfafa gwiwar kasa da kasa wajen dakile annobar COVID-19.

Samun ci gaba kafada da kafada shi ne ainihin ci gaba. A halin yanzu, kasar Sin na bakin kokarinta wajen taimakawa ci gaban duk duniya, bisa matakan zahiri da take dauka. Kana, kasar Sin wadda ke tsayawa haikan kan fadada bude kofarta ga kasashen waje, za ta kara samar da damammakin ci gaba ga kamfanonin kasa da kasa. (Murtala Zhang)