logo

HAUSA

Wang Qian: Yariniyar dake cike da fata kan makomarta duk da ke fama da wahalhalu

2021-11-10 16:33:26 cri

An haifi Wang Qian a wani karamin kauye dake cikin tsaunuka masu zurfi. Mahaifiyarta tana fama da tabin hankali, kuma tana iya ci da sha kawai, kanenta ya kamu da ciwon barnar kwakwalwa watanni 5 kacal da haihuwa, mahaifinta baya iya yin aiki saboda ciwon kashin baya na kasa sakamakon gajiya na dogon lokaci. Hakan ya sa Wang Qian ta dauki nauyin iyali. Amma wahalhalun ba su mamaye Wang Qian ba, ban da aiki, har ma ta kan shiga ayyukan sa kai, don taimakawa sauran mutanen dake bukatar.

An haife Wang Qian a wani iyali na musamman dake cikin dutse mai zurfi a birnin Liuan na lardin Anhui dake kudu maso gabashin kasar Sin. Tun lokacin da take da shekaru 6, Wang Qian ta soma kulawa da dan uwanta mara lafiya tare da mahaifinta. Mahaifiyarta tana fama da tabin hankali, kuma tana iya ci da sha kawai. A shekaru shida da suka wuce kuma, mahaifinta ba ya iya yin aiki saboda ciwon kashin baya na kasa.

A shekarar 2017, Wang Qian, wadda ta kammala karatu a kwalejin koyon ilmomin musamman ta hanyar samun kudin shiga a lokacin hutu, ta samu aikin yi a birnin Liu'an. Domin kulawa da iyalinta, sai Wang Qian ta dauke su a birnin, hakan dai ta dauki nauyin dukan iyali ita kadai.

Wang Qian: Yariniyar dake cike da fata kan makomarta duk da ke fama da wahalhalu_fororder_wangqian1

Gidan da Wang Qian ta yi hayar minti 5 ne kawai take bukatar zuwa wurin da take aiki ta hanyar hawan keke, amma duk da haka tana tsamanin akwai nisa a tsakanin wuraren biyu. Saboda a tsakar rana ta ko wace rana, bayan Wang Qian ta ci abincin aiki a dakin cin abinci na wurin aiki, sai ta hau motar batir kuma ta hanzarta zuwa gida don dafa wa mahaifiyarta da kanenta abincin rana. Saboda dukkansu sun iya cin taliya kawai. Bayan haka kuma, sai ta dauka kanenta a baya daga dakin kwana zuwa falo domin ta tamake shi wanka.

Kanenta yana da shekara 21 da haihuwa, kuma nauyinsa ya kai kusan kilogiram 65. Wang Qian ta ce, "Ya fi ni nauyi, kuma ba zan iya dauke shi ba nan gaba ba da dadewa ba."

Kanen ta ba ya iya magana, kuma idan ya yi rashin lafiya, sai ya jijjiga, da yanke kansa, har ma ya cuci wasu. Da take fuskantar nauyi daga iyali, da kuma kanen da kullum ke fama da rashin lafiya, Wang Qian bai taba yin gunaguni game da abin da ya faru a iyalinsu ba, balle ta yi kasala da iyalinta.

Wang Qian: Yariniyar dake cike da fata kan makomarta duk da ke fama da wahalhalu_fororder_wangqian3

A yayin da take fuskantar wahalhalu, Wang Qian ta samu taimako daga gwamnatoci bisa matakai daban daban da kuma mutane masu kirki da yawa. Tun daga shekarar 2015, iyalinta na ci gaba da samun kudin irin da aka samar na musamman ga mutanen da ke bisa matsayin zaman rayuwa mafi kankanta, da tallafin kudi na nakasassu bisa manufofin da batun da ya shafa, kuma sun yi zama a gidan haya na jama’a da gwamnatin kasar ta samar bisa kudi kadan kadan. Ban da wannan kuma, mutane masu kauna daga bangarori daban daban suna samar da kudi da kayayyakin taimako ga iyalinta. Dukkan kulawar da suka samu sun burge Wang Qian kwarai da gaske. Ta ce, Ko da yake iyalinta na fama da talauci, amma abin sa’a shi ne, suna zama a wani zamani mai kyau, manufofin kawar da talauci na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kulawa da gwamnatoci a matakai daban-daban da kuma dukkan bangarorin al'umma suka yi musu, sun ba da tabbaci ga mahaifinta, mahaifiyarta da kuma kanenta wajen ci gaba da zaman rayuwa da kuma samu jinya.

Irin wannan kirki da kauna daga al'umma, sun taimakawa Wang Qian don ci gaba da zaman rayuwarta, a sa'i daya kuma, sun sanya ta haifar da ra'ayin shiga ayyukan jinkai don sadaukar da al'umma. Ta ce, “Saboda ruwan sama ya taba kame ni, ni ma ina son in rike laima ga wasu.” Ta shiga cikin kungiyoyin sa kai da dama, ko dai na rigakafin da shawo kan annobar COVID-19 ko kuma ba da agajin ambaliyar ruwa, Wang Qian za ta ba da lokaci don yin iyakacin kokarinta wajen taimakawa masu bukata. A watan Afrilu na shekarar 2020, Wang Qian kuma ta yi rajista a matsayin mai ba da gudummawar gabobin jiki.

Wang Qian: Yariniyar dake cike da fata kan makomarta duk da ke fama da wahalhalu_fororder_wangqian2

Wahalhalun da take sha kan zaman rayuwa bai mamaye mafarkin Wang Qian ba. Bayan kula da kanenta da mahaifiyarta a kowace rana, Wang Qian tana nacewar yin karatu. Da dare, Wang Qian za ta bude littafi, wannan lokacin shi ne lokacin da ta fi jin dadin hankalinta.

Bayan shekara biyu da rabi tana aiki tukuru, ta cimma nasarar samun digiri na farko na jami’a. Dagewa wajen koyon ilmi ba wai kawai ya sa ta ji gamsuwa a zuciyarta ba, har ma ya sa ta cike da fata kan makomarta ta nan gaba. Wang Qian ta ce, burinta shi ne ta zama wata malama, wannan kuma shi ne "haske" a cikin rayuwarta. Kullum tana fatan kanenta zai iya kiranta 'yar uwar a wata rana, za kuma ta dawo shi zuwa duwatsu ko wasu wurare masu nisa don gudanar da aikin koyarwa. A lokacin, za ta yi amfani da gogewarta ta gaya wa yaran da ke wurin cewa, ya kamata su yi jajircewa, da nuna kwazo, dole ne su yi karatu, hakan za su fita waje don su sani cewa, duniyar da ke wajen dutsen tana da girma kuma akwai mutanen kirki da yawa.