logo

HAUSA

Jakadan Sin a Najeriya ya gana da uwargidan shugaban kasa

2021-11-10 20:35:05 CRI

Jakadan Sin a Najeriya ya gana da uwargidan shugaban kasa_fororder_AA

A ranar Litinin ne jakadan kasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya gana da uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari. Yayin zantawar su Mr. Cui ya ce cikin shekaru sama da 50, bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Najeriya, alakar sassan biyu ta ci gaba da zurfafa bisa daidaito.

Jakada Cui ya ce tsagin Sin ya jinjinawa kwazon uwargida Aisha Buhari bisa gudummawar ta, yana mai cewa Sin na dora muhimmancin gaske ga alakar ta da Najeriya, tana kuma aiki tare da Najeriya domin zurfafa hadin gwiwa a dukkanin sassa, tare da kokarin daga darajar alakar su yadda ya kamata.

A nata tsokaci kuwa, Aisha Buhari cewa ta yi annobar COVID-19 na ci gaba da addabar duniya, kuma mata da kananan yara a Najeriya na fuskantar karin kalubale a fannin kare hakkoki da muradun su. Ta ce Najeriya a shirye take ta karfafa tattaunawa, da tsara ayyuka tare da Sin, domin ingiza alakar sassan biyu ta fuskar raya kiwon lafiyar al’umma, da ilimi da sarrafa albarkatun noma, da kuma kara samarwa al’ummun kasashen biyu alherai.  (Saminu)