logo

HAUSA

Bai Dace A Siyasantar Da Gasar Olympics Ba

2021-11-10 16:23:31 CRI

Bai Dace A Siyasantar Da Gasar Olympics Ba_fororder_1110-01

Yayin da kasar Sin ta kammala dukkan shirye-shirye da suka wajaba, don gabatarwa duniya kasaitacciyar gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022, da birnin Beijing zai karbi bakunci, sai kuma ga shi tun ba a je ko’ina, kasar Amurka ta fara nuna halinta ne neman siyasantar da gasar, inda a kwanakin baya ta bukaci kasar Sin da wai kada ta takaita 'yancin zirga-zirga ga 'yan jaridu a lokacin wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, tare da tabbatar da kare lafiyarsu da 'yancin bayar da rahotanni. Hali aka ce zanen dutse.

Rahotanni na nuna cewa, yanzu haka 'yan jarida fiye da 2,500 ne suka mika takardarsu na neman rajista, don watsa rahotanni game da gasar Olympics ta lokacin sanyi ta birnin Beijing. Don haka, wannan batu da Amurka ta gabatar bai ma taso ba.

Kasar Sin dai ta sha nanata cewa, tana maraba da 'yan jaridu, da su rika ba da rahoto kan gine-ginen wuraren wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, da shirye-shiryen gasar, da tabbacin gudanar da aiki da sauran ayyukan da ke da alaka da su, da kuma gudanar da aikin sa ido, wanda zai taimaka matuka wajen inganta tsari da gudanar da wannan gasa cikin armashi.

Sai dai kuma, kasar Sin dai ta yi kakkausar suka ga yadda wasu kasashe ke neman siyasantar da wasannin motsa jiki, da akidar nuna kyama ga kasar Sin, da kirkirar labarai da bayanan karya da ke bata sunan kasar Sin da wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing da sunan 'yancin 'yan jarida.

Yanzu haka ma,kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya IOC, ya yi matukar yabawa kasar Sin bisa cika alkawarinta na gudanar da wasanni ba tare da gurbata muhalli ba, ta hanyar amfani da makamashi masu tsafta a wuraren wasannin, tare da jan hankalin masoya wasannin lokacin hunturu miliyan 300.

Masu fashin baki na cewa, duk mai son halartar duk wata gasa a ko’ina a duniya, wajibi ne ya martaba dokoki ka ka’idojin da aka tanada daga dukkan fannoni, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu. (Ibrahim Yaya)