logo

HAUSA

Cutar kwalara ta karbe a yankin kudu maso yammacin Kamaru

2021-11-10 10:17:25 CRI

Kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar Sin, ya hakaito daga shafin yanar gizo na kasar Kamaru cewa, an samu karuwar masu kamuwa da cutar kwalara cikin makonni biyu da suka gabata a yankin kudu maso yammacin kasar, lamarin da ya kara jefa al'umma cikin mawuyacin hali tare da karuwar masu kamuwa da cutar ta COVID-19.

Wani rahoto da wakilan lafiyar jama'a na yankin kudu maso yammacin kasar suka bayar, ya bayyana a jiya Talata cewa, mutane 5 sun mutu, kana an tabbatar da mutane 32 da suka kamu da cutar a yankin.

Rahoton ya ce, jami'ai na fuskantar kalubale na kudi, da kayan aiki da wadanda dan Adam ke haddasawa, don ci gaba da ayyukan dakile cutar.

Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD (OCHA), ya bayyana a shafinsa na Tiwita cewa, annobar ta barke a yankin kudu maso yammacin kasar, a gabar da ake fama da yanayi na rashin tsaro da matsalolin jin kai, ga kuma yadda jama’a suka koma harkokinsu na zirga-zirga zuwa wuraren da ba su da tsaftataccen ruwan sha da kuma wuraren bahaya,   

Cutar kwalara, cuta ce da ake saurin kamuwa da ita, a mafi yawan lokuta ta kan haddasa barkewar gudawa tsaroro ba kakkautawa, wanda kan kai ga mutuwa sakamakon rashin ruwa a jikin wanda ya kamu da ita.(Ibrahim)