logo

HAUSA

Nazarin nasarorin da JKS ta cimma cikin shekaru 100 domin neman karin ci gaba nan gaba

2021-11-10 09:33:33 CRI

A wannan mako ne, aka kira taro na 6 na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19 a gabar da jam’iyyar ke cika shekaru 100 da kafuwa a wannan shekara. Jami’iyyar da ta fara da mambobi kalilan, yanzu ta kasance jam’iyya mafi yawan mambobi da girma a duniya. Haka kuma JKS ta zama jam’iyyar da ta yi nasarar jagorantar al’ummar Sinawa wajen tsame baki dayan jama’arta daga kangin talauci, cikin wani wa’adi da ya baiwa duniya mamaki matuka.

Nazarin nasarorin da JKS ta cimma cikin shekaru 100 domin neman karin ci gaba nan gaba_fororder_211110世界21042-hoto2

A yayin wannan zama ne kuma, babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping, ya gabatar da rahoton aiki a madadin hukumar siyasar kwamitin koli, ya kuma yi bayani kan daftarin kudurin kwamitin tsakiyar JKS game da manyan sakamako da fasahohin tarihi da JKS ta samu a cikin wadannan shekaru 100 da suka gabata.

Sai dai a yayin da kasar Sin da daukacin al’ummar Sinawa ke murnar cikar wannan babbar jam’iyya shekaru 100 da kafuwa, da ma tarin nasaroin da kasar ta cimma karkashin jagorancinta, wasu kasashen yamma da ’yan kanzaginsu, na nuna adawa da manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma, har ma suke neman bata sunanta da yada karaikayi kan wasu manufofi da take dauka a wasu yankunanta, don neman cimma burinsu na siyasa.

Kadan daga cikin irin wadannan nasarori, sun hada da fitar da al’umma daga kangin talauci, gina al’umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, dakile yaduwar annobar COVID-19 da samar da alluran riga kafin cutar. Sauran sun hada da nasarar a fannin binciken sararin samaniya, fannin fasahohin kimiya da na kirkire-kirkire, da sauransu.

Nazarin nasarorin da JKS ta cimma cikin shekaru 100 domin neman karin ci gaba nan gaba_fororder_211110世界21042-hoto3

Har kullum kasar Sin tana kira a martaba zabin kasashe na samun bunkasuwa da ya dace da yanayin da suke ciki, da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe, da martaba ka’idar alakar kasa da kasa, ta yadda za a gina al’ummma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama..

A cikin shekaru 100 da suka gabata, JKS ta shaida ta hanyar daukar hakikanin matakai cewa, ita jam’iyya ce mai kishin zaman lafiya da neman ci gaba, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, da bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, da kuma raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama yayin da take daidaita harkokin kasa da kasa abin da masu fashin baki ke cewa, JKS za ta kara jagorantar al’ummar Sinawa, wajen cimma tarin nasarori na ban-al’ajabi a duniya a nan gaba. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)