logo

HAUSA

Waiwaye Adon Tafiya

2021-11-09 19:37:33 CRI

Waiwaye Adon Tafiya_fororder_1109-1

A farkon wannan makon ne kwamitin tsakiya na Jam’iyyar kwaninis ta kasar Sin ya fara cikakken zamansa karo na 6, inda ake ganin zaman zai kasance mai muhimmanci wajen saita alkiblar da kasar za ta dauka a nan gaba.

Yayin da a bana aka cika shekaru 100 da kafuwar Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping, ya gabatar da wani daftari dake kunshe da nasarori da darussan da jam’iyyar ta dauka cikin shekarun 100.

Masu iya magana na cewa, waiwaye adon tafiya, wato idan ana son tafiya ta gaba ta yi kyau, dole ne a nazarci wadda aka yi a baya. Lallai wannan daftari zai  tabbatar da an kawar da duk matsalolin da aka gamu da su. Kalubale da walhalhalu, har ma da nasarorin da aka gamu da su cikin wadancan shekaru, za su kasance kyawawan darasi da kasar Sin za ta yi amfani da su, domin ta nan ne za ta kara samun gogewa da kuma kyawawan dabaru da za su kai ga samun karin nasarori na azo a gani.

Shaidu sun riga sun tabbatar da ire-iren nasarorin da irin wannan daftari da shi ne irinsa na 3 da aka gabatar a kasar Sin suka samar. Kasancewar daftarorin na baya, sun taka muhimmiyar rawa wajen karfafa jam’iyyar da samar da hadin kai a tsakanin mambobinta da kuma haifar da kyawawan sakamako, babu makawa hakan ce za ta kasance da wannan sabon daftari, a wannan lokaci da wasu sassan duniya ke kara nuna adawa da kishi da ci gaban kasar Sin, wannan daftari zai karfafa jam’iyyar da kai ta ga matsayin da ba a gani ba a baya, tare da amfanawa dimbin jama’ar kasar Sin kamar ko da yaushe.

A ganina, irin wannan waiwaye da kasar Sin ke ci gaba da yi, daya ne daga sirrin kanta na samun ci gaba. Haka kuma shi zai tsara mata hanyoyin da za ta bi wajen kare kanta daga duk wata matsala ko barazana a wannan lokaci. Har kullum kasar Sin na samar da darasi ga duniya, zan iya cewa, wannan mataki da Sin ta dauka, abu ne mai muhimmanci da ya kamata a yi koyi da shi. Ya kamata kasashen duniya su nazarci tarihi da darussan da suka koya a baya, domin saita alkiblar da ta dace ga ci gaban kasashensu da al’umma. (Fa’iza Mustapha)