logo

HAUSA

Senegal ta sha alwashin gudanar da taro na 8 na ministocin dandalin FOCAC cikin nasara

2021-11-09 20:50:28 cri

Senegal ta sha alwashin gudanar da taro na 8 na ministocin dandalin  FOCAC cikin nasara_fororder_0658b5f4f627463aa584f4fa95a937a0

Ministar harkokin wajen kasar Senegal Aissata Tall Sall, ta ce kasarta ta kudiri aniyar gudanar da taro na 8, na ministocin kasashe mambobin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC cikin nasara.

An dai tsara gudanar da wannan taro ne tsakanin ranekun 29 zuwa 30 ga watan nan na Nuwamba a birnin Dakar.

Da take tsokaci game da taron, yayin zantawar baya bayan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, uwargida Sall ta ce dandalin FOCAC na da nufin yin aiki tukuru cikin shekaru 3 masu zuwa, a fannin tabbatar da cimma nasarori bayan wucewar annobar COVID-19.

Jami’ar ta ce kasashen Afirka, za su ganewa idanun su karkon manufofin kasar Sin game da jurewa yanayin tattalin arziki, da tallafin lafiya, bayan wucewar annobar, yayin da a daya hannun Sin din ke ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, domin karfafa hadin gwiwar ta da kasashen Afirka.

Sall ta kuma yi imanin cewa, Sin za ta ci gaba da zama abun misali ga kasashe irin su Senegal, da ma sauran sassan nahiyar Afirka. Ta ce Sin ta cancanci yabo, bisa nasarar musamman da ta cimma, a fannin raya tattalin arziki da bunkasa zamantakewar al’ummun ta.   (Saminu)