logo

HAUSA

Yara 21 sun rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan renon yara dake kudancin Nijar

2021-11-09 10:17:49 CRI

Jiya Litinin ne, wata gobara ta tashi a cikin wani gidan renon yara kanana a yankin Maradi dake kudancin kasar Nijar, inda a kalla mutane 21 suka rasa rayukansu.

Wasu rahotanni da kafofin watsa labaran kasar ta Nijar suka bayar sun nuna cewa, da safiyar jiya ne, gobara ta tashi a cikin wani gidan renon yara kanana da aka gina da ciyayi a yankin Maradi ba zato ba tsamani, inda yara 21 suka rasa rayuka, wasu 19 suka ji rauni, kana 9 daga cikinsu sun ji rauni mai tsanani, ana kuma fargabar adadin mutanen da suka mutu zai iya karuwa.

Har zuwa wannan lokaci dai, gwamnatin Nijar ba ta sanar da dalilin tashin gobara ba.(Jamila)