logo

HAUSA

Mace da ta sauya matsayi daga mai kiwon tumaki zuwa malamar jami'a ke nan

2021-11-08 12:35:59 cri

Mahmooda Taqwa Milad, wadda ta shafe kuruciyarta a wani kwari da ake kira Do Ab a jihar Vardak dake tsakiyar kasar Afghanistan. Mazauna kauyen sun yi mata lakabi da “Yarinyar da ke zuwa makaranta”. Amma, bisa kokarin da ta yi, ta zama malama a jami’a daga wata mai kiwon tumaki.

A yau Taqwa malama ce a Jami'ar Kabul, inda ta riga ta samu digiri na biyu, tana koyar da yare da adabi na Pashto. Tana koyar da daliban aji guda uku a ko wace rana, ko wane aji dake da dalibai a kalla 50. Tana amsa ko wace tambaya daga dalibai ta hanyar amfani da manhajar hira. Ko da yake ta kasance mai shan aiki, ta yadda har ba ta iya amsa sakon sauran mutane, amma tabbas sai ta amsa sakon dalibanta. Tana daukar dalibanta kamar abokanta, kuma ko da yaushe tana kokarin taimaka wa dalibai mata.

Da take magana game da ra’ayinta kan aiki, Taqwa ta kawo mana wani labari, ta ce, akwai wani tsoho manomi mai saje a kauyen su, yana da kusumbi kuma yana tafiya cikin rawar jiki. Akwai wani karamin tsiro a bankin kogin, kuma yana bashi ruwa a kowace rana. Taqwa ta tambaye mahaifinta cewa, me ya sa wannan tsoho yake kulawa da karamin tsiro, akwai wahala sosai. Mahaifinta ya ce, 'Ya'yan itacen da suke ci yanzu shi ne ‘ya'yan itacen da kakansu ya dasa a da, ko da yake kaka ya riga mu gidan gaskiya, amma har yanzu ana iya cin ‘ya’yan itacen, haka duniyarmu take, idan mutane suna taimakawa juna, za a sami yiwuwar yin abubuwa masu yawa. Lokacin da muke yin wani abu, bai kamata mu yi la’akari da kanmu kadai ba, ya kamata mu yi tunanin wasu.

Mace da ta sauya matsayi daga mai kiwon tumaki zuwa malamar jami'a ke nan_fororder_4

Yanzu Taqwa tana da shekarun 33, ta riga ta samu digiri na biyu, a matsayinta na wata malama a jami'a, ta kuma buga littattafai guda biyu. Ta yi aure, amma ba ta da 'ya'ya, Taqwa ta ce, mijinta bai karfafa gwiwarta ba a fannin aiki, amma a kalla bai tsoma baki cikin aikin ta ba. Game da haka, Taqwa ta amince da cewa, idan aka kwatanta da yawancin matan Afghanistan, babu abin da za ta yi korafi akai. Ta ce, ta kan tuna da ‘yan mata masu shekara daya da ita a kauyensu. Sun riga sun yi aure kuma akwai bukatar su yi aikin gida da kula da ‘ya’yansu, watakila suna fama da talauci. A cewar Taqwa, idan aka kwatanta da su, Allah ya ba ta sa’a sosai. Ko da yake ta samu nasara ne sakamakon namijin kokarin da take yi, amma akwai dubban 'yan mata da ke aiki tukuru kamar ita, amma watakila ba za su iya cimma burinsu ba.

Taqwa ta kara da cewa, idan aka kwatanta da matsayin mata da maza a kasar Afghanistan da na wasu kasashe, har yanzu akwai doguwar hanya wajen daidaita bambancin matsayin. Ta ce, "Idan wata mace tana bin hanyar da ta dace a wata kasa, mai yiwuwa tana iya cimma burin ta cikin sauki. Amma a Afghanistan, kuma ga al’ummar Pashtun, samun ilimi ya kasance wani abu ne mai wuya sosai ga mata. "

‘Yan matan Afganistan da yawa suna yin ayyukan gida da yawa, amma duk da haka suna iya samun maki mai kyau a fannin karatu. Mene ne dalilin ? Saboda suna damuwa idan ba su yi amfani da wannan dama ba, wata rana mijinsu, mahaifinsu ko dan'uwansu zai ce kada su je makaranta, za a kwace ‘yancinta na samun ilmi.

A sakamakon haka, wannan malama 'yar Afganistan da ta cire mayafinta kuma ta kwantar da hankalinta a yayin da take fuskantar ‘yan jaridarmu wato ta wata kasar waje, ta yi kira da cewa, kada mata su rasa niyyarsu, kada su yi watsi da halatattun hakkokinsu, kuma ko da yaushe su yi kokari don samun ‘yanci da moriyarsu.

Mace da ta sauya matsayi daga mai kiwon tumaki zuwa malamar jami'a ke nan_fororder_2

Kwanan nan sashen ilimi na Taliban na Afghanistan, ya fitar da wata takarda da ke bukatar matan da ke yin rajista a jami’o’i masu zaman kansu, da su sanya dogayen riguna da mayafin da zai iya rufe yawancin fuskokinsu. Kana kuma dole ne mata su koyar da dalibai mata, amma idan hakan ba zai yiwu ba, an amince dattawa masu dabi’a mai kyau su koyar da su.

Bugu da kari, ya kamata a raba dalibai maza da mata a aji, ko kuma a kalla a raba su da labule. Kaza lika wajibi ne daliban su rika amfani da hanyoyin shiga da na fita daban daban. Baya ga haka, ya kamata dalibai mata su bar aji mintuna 5 kafin dalibai maza su tashi daga aji, don gujewa haduwarsu.

Ko da yake yanayin da aka ambata yana da tsanani, duk da haka ya kasance wani babban ci gaba, idan aka kwatanta da ka'idodin da kungiyar ta aiwatar a lokacin gwamnatin ta shekaru 20 da suka gabata. Wato a wancan lokaci "ba a yarda da mata su shiga cikin rayuwar jama'a da ayyukan nishadi ba".

An baiwa mata "masu ilmi" kamar su Taqwa dama ta dan lokaci, to amma yaya abun yake ga dunbin mata dake kasar ? Ka’idodin da suka shafi wai dole malamai mata su koyar da dalibai mata, da matsalar karancin malamai mata, sun sanya yara mata da yawa rasa damar shiga makaranta, wanda hakan zai haifar da karin matsalar rasa isassun malamai mata... hanyar warware wannan matsala, babban batu ne da sabuwar gwamnatin Afghanistan ke fuskanta.