logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin ya shigo shekarar 2021 da kafar dama

2021-11-08 18:19:24 CRI

Tattalin arzikin Sin ya shigo shekarar 2021 da kafar dama_fororder_1108-1

Duk da kasancewar har yanzu kasashen duniya na cigaba da yaki da cutar numfashin ta COVID-19, sannan a hannu guda ana ta kokarin lalibo hanyoyin farfado da tattalin arzikin duniya wanda annobar ta yiwa mummunar illa, zamu iya cewa, a bisa dukkan alamu tattalin arzikin kasar Sin ya shigo shekarar 2021 na kafar dama. Koda yake, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen yaki da annobar COVID-19 har ta samu manyan nasarori, sannan ba ta yi kasa a gwiwa wajen daukar matakan farfado da tattalin arzikinta da ma na duniya ba. A karshen wannan mako, alkaluman da hukumomi suka fidda ya nuna cewa, jimillar hada-hadar kasuwancin shigi da fici na kasar Sin ya karu da kashi 22.2 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara inda ya kai yuan triliyan 31.67 kwatankwacin dala triliyan 4.89 a watanni 10 na farkon wannan shekara ta 2021. A cewar babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, adadin ya karu da kaso 23.4 idan an kwatanta da na shekarar 2019 wato tun gabanin barkewar annobar COVID-19. Bisa alkaluman hukumar kwastam din, bangarorin biyu na shigi da ficin, duka sun ninka adadinsu a watanni 10 na farko na wannan shekara, inda suka karu da kashi 22.5 da kuma kashi  21.8 bisa 100 idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata. Bugu da kari alkaluman sun nuna cewa, a watan Oktoba kadai, adadin shigi da ficin kasar Sin ya karu da kashi 17.8 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara. Koda yake, wannan gagarumar nasarar ta dogara ne bisa ga jajircewa da tsayawa tsayin daka da mahukunta kasar ke yi don ganin haka ta cimma ruwa. Alal misali, koda a makon da ya gabata, yayin da ya halarci bikin bude taron baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na hudu, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada cewa, kasar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen kiyaye tsarin huldar kasa da kasa da musayar damammakin kasuwanci da sauran sassan duniya da inganta bude kofa da tsare muradun bai daya na duniya ba. Sannan shugaban ya nanata cewa, duk da kasancewar har yanzu ana fama da annobar COVID-19, kuma farfadowar tattalin arzikin duniya na fuskantar tarnaki. Don haka akwai bukatar al’ummun dukkan kasashe su taimaki juna wajen shawo kan matsalolin tare. Ya ce a shirye kasar Sin take ta hada hannu da sauran kasashe wajen gina tattalin arzikin duniya. Dama dai masu hikimar magana na cewa, “zomo ba ya kamuwa daga zaune.” (Ahmad Fagam)