logo

HAUSA

ECOWAS ta azawa gwamnatin rikon kwaryar Mali takunkumi

2021-11-08 09:46:56 CRI

ECOWAS ta azawa gwamnatin rikon kwaryar Mali takunkumi_fororder_211108-ECOWAS Mali-Ahmad1

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), a ranar Lahadi ta sanyawa hukumomin gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali takunkumi a matsayin martani game da ikirarin da suka yi cewa ba za su iya cika wa’adin mika mulki ta hanyar shirya zabe a watan Fabrairun shekarar 2022 ba.

A sanarwar bayan taron da aka fitar, bayan kammala zama na uku na babban taron shugabannin kasashe da gwamnatocin mambobin ECOWAS wanda aka shirya game da batutuwan siyasar Mali da Guinea, sanarwar ta ce takunkuman sun hada da na hana tafiye tafiye da rufe asusun ajiyar kudade da kaddarori.

Sanarwar wanda shugaban gudanarwar kungiyar ECOWAS, Jean-Claude Kassi Brou, ya karanta, ya bayyana cewa, ECOWAS ta yanke shawarar kakaba takunkumin ba tare da bata lokaci ba kan daidaikun mutane da kungiyoyi wadanda aka tantance su, da suka hada da dukkan mambobin hukumomin gwamnatin rikon kwaryar, da iyalansu, da sauran cibiyoyin gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Sanarwar bayan taron ta kuma umarci shugaban ECOWAS da ya sake duba yiwuwar saka karin wasu takunkuman a babban taron kungiyar dake tafe a watan Disamba, muddin al’amurra suka cigaba da kara tabarbarewa. (Ahmad)