CIIE Na Taimakawa ’Yan Afghanistan Sayar Da ’Ya’yan Itacen Pine A Sin
2021-11-08 21:55:42 CRI
A daren ranar 6 ga wata, cikin shagon yanar gizo na babban gidan rediyon da talabijin na kasar Sin (CMG) a bikin CIIE, wato bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na hudu a birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin, an sayar da dukkanin ‘ya’yan itacen pine kwalabe guda dubu 120 cikin ‘yan mintuna.
An shigo da wadannan ‘ya’yan itacen pine daga kasar Afghanistan, kuma, gaba daya, kasar Sin ta shigo da ‘ya’yan itacen pine ton dubu 450 daga kasar Afghanistan. Bisa labarin da aka samu, an ce, bana, an girbi ‘ya’yan itacen pine da kyau a Afghanistan, amma, aka gamu da matsalar sayar da su, sabo da matsalar yaduwar annobar cutar COVID-19 a kasar da halin da ake ciki a wurin.
Yadda aka sayar da dukkanin ‘ya’yan itacen pine kwalabe dubu 120 a bikin CIIE ya nuna cewa, lallai, an kafa dandali mai kyau ga kasashe marasa ci gaba na sayar da kayayyakinsu, ya kuma nuna aniyar kasar Sin wajen kare tsarin ciniki a tsakanin sassa daban daban, da kuma raya kasuwannin kasa da kasa cikin hadin gwiwa. Kuma, “Hadin Gwiwa” shi ne babban taken bikin CIIE.
A bana, kimanin kamfanoni kimanin 90 daga kasashe mafi fama da talauci guda 33 sun halarci bikin, kuma, kasar Sin ta samar musu dandali kamar yadda suke bukata.
Kasar Sin ta kaddamar da bikin CIIE kamar yadda aka tsara, domin samar da damammaki ga kasa da kasa cikin yanayin adalci, da kuma inganta bunkasuwar kasa da kasa bisa ka’idojin nuna adalci, da fahimtar juna, da tallafawa kowa da kowa, da kuma hadin gwiwa, lamarin da ke da muhimmanci sosai wajen neman farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)