logo

HAUSA

Rwanda ta karbi kaso na biyu na rigakafin COVID-19 daga kasar Sin

2021-11-08 11:24:40 CRI

Rwanda ta karbi kaso na biyu na rigakafin COVID-19 daga kasar Sin_fororder_211108-Rwanda-Ahmad3

A ranar Lahadi, kasar Rwanda ta karbi gudunmawar alluran riga-kafin COVID-19 guda 300,000 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin, wanda gwamnatin Sin ta bayar, kuma wanan shi ne karo na biyu da kasar Sin ta baiwa Rwanda gudunmawar alluran riga-kafin.

Albert Tuyishime, shugaban sashen yaki da cutuka masu yaduwa na cibiyar nazarin magunguna ta kasar Rwanda ya bayyana cewa, sun yi farin cikin samun kaso na biyu na alluran riga-kafin wanda hakan alamu ne dake nuna hadin gwiwa da kuma goyon bayan da gwamnatin kasar Sin take baiwa Rwanda a yakin da take da annobar COVID-19.

A cewar jami’in, tun bayan barkewar annobar COVID-19, kasar Rwanda take yin aiki tare da gwamnatin kasar Sin ta fannin samar da kayayyakin gwaje-gwajen cutar, da jiyyar masu fama da cutar gami da samar da riga-kafin cutar. (Ahmad)