logo

HAUSA

Sharhi: Kiyaye makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka

2021-11-07 21:46:17 CRI

Sharhi: Kiyaye makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka_fororder_321

A ranar 5 ga wata, an gudanar da taron dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka ta fannin tsarin BDS karo na farko a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda sassan biyu suka tattauna batun fadada hadin gwiwarsu wajen gudanar da tsarin BDS da ma harkokin sararin samaniya.

Tsarin BDS wato tsarin jagorantar zirga-zirga bisa taimakon tauraron dan Adam na Beidou, na daya daga cikin manyan tsarukan jagorantar zirga-zirga guda hudu na duniya. Ya zuwa yanzu, ana amfani da tsarin a kasashen Afirka 34.

Binciken sararin samaniya na daya daga cikin muhimman fannonin da Sin da Afirka ke gudanar da hadin gwiwarsu. Kasashen Afirka da dama na da burin bunkasa harkokin sararin samaniya, don fanin ganin kyautata karfinsu na sadarwa da ma sauran harkoki na zamani, sai dai suna fuskantar wasu matsalolin da ke yi musu tarnaki. Kasar Sin a nasa bangare, a yayin da take kokarin bunkasa kimiyyar binciken sararin samaniya, ba ta manta da kawayenta na Afirka ba, inda take bin hanyoyi daban daban wajen taimaka musu cimma burinsu. Don haka kuma, kimiyyar binciken sararin samaniya na kara taka rawar gani wajen inganta ci gaban tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma a kasashen Afirka.

Sharhi: Kiyaye makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka_fororder_微信图片_20211107211013

Ranar 14 ga watan Mayun shekarar 2007 muhimmiyar rana ce da ba za a manta ba a tarihin binciken sararin samaniya na kasar Nijeriya. A wannan rana, kasar Sin ta harba tauraron dan Adam na sadar na farko na kasar zuwa falakin da aka tsara, tauraron da ya biya bukatun kasa ta fannin sadarwa da rediyo da yanar gizo da dai sauransu. Baya ga haka, tauraron yana kuma iya samar da hidimomi ga kasashen da ke makwabtaka da Nijeriya, wanda ya sa kaimin harkokin sadarwa a nahiyar Afirka. Tauraron ya kasance na farko da kasar Sin ta taimakawa kasashen Afirka harbawa, wanda kuma ya bude babin hadin gwiwar sassan biyu a fannin binciken sararin samaniya.

Sinawa kan ce, koya wani aikin kama kifi ya fi a ba shi kifi kai tsaye. Ba kawai kasashen Afirka ke son mallakar taurarin dan Adam nasu, suna kuma da niyyar bunkasa ayyukan bincike da samar da taurarin dan Adam. Don haka, a cikin ‘yan shekarun baya, Sin da kasashen Afirka na fadada hadin gwiwarsu a fannonin nazarin taurarin dan Adam da kuma samar da su, matakin da ya inganta karfin kasashen Afirka wajen bunkasa harkokin sararin samaniya. A shekarar 2016, Sin da Masar sun daddale yarjejeniyar gina cibiyar harhada taurarin dan Adam da gwajinsu a Masar, yarjejeniyar da aka fara aiwatarwa a shekarar 2017, ana kuma sa ran Masar za ta samu cibiyar harhada taurarin dan Adam da gwajinsu ta farko bayan kammala aikin.

Sharhi: Kiyaye makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka_fororder_3817827

Ci gaban harkokin sararin samaniya ba su iya rabuwa da kwararru. Don haka, kasar Sin tana kuma kokarin taimaka wa kasashen Afirka wajen horar da masanan binciken kimiyyar sararin samaniya. Daidai kamar yadda Ahcene Boukhelfa ya fada, dalilin da ya sa muke hadin gwiwa da kasar Sin shi ne kasar Sin tana ba mu fasaha da horar da kwararrunmu, baya ga kuma yadda ta fi wasu kasashe ta fannin fasaha da farashi.

A watan Satumban shekarar 2018, an gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a birnin Beijing. A gun bikin bude taron, shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ya gabatar da jawabi, inda ya jaddada hada kan Sin da kasashen Afirka, don kiyaye makomarsu ta baki daya. Kuma a hakika, nasarorin da aka cimma ta fannin hadin gwiwar sassan biyu wajen harkokin binciken sararin samaniya sun bayyana ainihin ma’anar kiyaye makomar bai daya a tsakanin Sin da Afirka.

A karshen wannan wata, za a gudanar da taron ministoci karo na takwas na dandalin a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal, kuma babu shakka, taron zai taimaka ga ciyar da hadin gwiwar sassan biyu ta fannoni daban daban gaba, don kiyaye makomarsu ta bai daya.(Lubabatu)