logo

HAUSA

UNHCR ta kwashe bakin haure 172 daga Libya zuwa Nijer

2021-11-07 16:37:02 CRI

UNHCR ta kwashe bakin haure 172 daga Libya zuwa Nijer_fororder_a04-UNHCR evacuates 172 vulnerable asylum

Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), ta sanar a ranar Juma’a cewa, ta kashe bakin haure dake neman mafaka 172 daga kasar Libya zuwa Nijer.

UNHCR, hukuma ce dake lura da ’yan gudun hijira ta MDD, ta yi nasarar kwashe mutane 172 dake gararamba daga kasar Libya zuwa jamhuriyar Nijer da yammacin ranar 4 ga watan Nuwamba. Wannan shi ne karon farko da hukumar ta kwashe mutane ta jirgin sama zuwa Nijer, sama da shekara guda, bayan da hukumomin kasar Libyan suka dage dokar dakatar da aikin jinkan bil adama na kwashe mutane ta jiragen sama, kamar yadda hukumar ta UNHCR ta bayyana.

Aikin kwashe mutanen ya gudana ne ta hanyar wani shirin sufuri na gaggawa wanda aka kafa a shekarar 2017 tare da taimakon gwamnatin Nijer, wanda kasar ta amince bisa wani tsarin wucin gadi na karbar ’yan ci rani wadanda rayuwarsu take cikin hadari a Libya.

Kawo yanzu, ’yan gudun hijira da masu neman mafaka 3,361 aka kwashe daga Libya zuwa Nijer, sannan 3,213 daga cikinsu tuni sun bar Nijer din zuwa kasashensu don cigaba da zaman rayuwa. (Ahmad)